January 31, 2023

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Ƴan siyasa ku guji amfani da mimbarin Wa’azi domin biyan bukatar ku – Abdulkarim Tilde

Page Visited: 114
0 0
Read Time:1 Minute, 31 Second

Daga Muhammad Sani Abdulhamid

 

Anyi kira wa ƴan siyasa da su dena amfani da mimbarin wa’azi don neman biyan bukatun su na siyasa.

Abdulkarim Sa’ad Tilde, Shugaban Kungiyan Haske Neighborhood Tilden Fulani, karamar hukumar Toro shi yayi wanan kira yayi wata hira da manema labarai kan irin mutumin da Yakamata Al’ummar karamar hukumar Toro su zaba matsayin wakilin su.

Abdulkarim Tilde yace kamata yayi al’umma su zabi mutum da yake da ilimi na siyasa Dana kasuwanci Wanda Kuma zai iya tafiya da kowa bayan hawan sa mulki. ” irin wadannan mutane sune ya kamata mu dinga bawa dama domin su wakilce mu a bangare daban daban na siyasance.”

“Ƴan siyasa ku guji amfani da mimbari na jumma’a domin biyan bukatar ku, mimbari wajen Isar da sakon Allah ne, wasu yan siyasa na amfani da mimbari ne wajen raba Kan Al’umma Kuma dukkan masu yin Haka su tuba su daina kafin fishin Allah ya sauka akansu.”

Shugaban sai ya jawo hankalin matasa da su kula da ire iren cigaban da ‘yan siyasa ya kamata su dinga kawowa, ba Wai mutum ya kawo “street lights” kokuma “transformers” shine ya kawo cigaba ba, akwai abubuwa masu yawa da dan siyasa ya kamata ya dinga mawa matasa domin cigaban rayuwar su.

Abdulkarim Tilde, sai yayi kwatance da wani Dan Kasuwa Hon. Ismael Dabo Wanda yayi amfani da dukiyar sa, karfinsa, ilimin sa tare da lokacin shi wajen ganin matasan karamar Hukumar Toro sun samu abin dogaro da kansu.

“Shi wannan mutumin Dan Kasuwa ne Wanda babu wata kujeran mulki a hanunshi, yanzu ne yake nema, ina kira wa matasa da iyaye Mata da mu tsaya muyi zabe me amfani, mu zabi Hon Ismael Dabo wato Talban Toro domin cancanta, nagarta, ilimi da Kuma kawowa Al’umma cigaba, domin irin ayyukan da yakeyi yasa muka fito don yada manufar shi.”

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *