Jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Akwa Ibom sun kama wasu mutane biyu a wurare daban-daban, bisa zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, a ƙananan hukumomin Ibeno da Eket.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar DSP Timfon John wadda ya bayyana hakan a ranar Lahadi ya bayyana cewa “lamarin farko ya faru ne a ranar 22 ga watan Fabrairu 2025, da misalin karfe 11:00 bayan samun bayanan sirri daga wani ɗan ƙasa mai bin doka, wanda ya nuna cewa wani mutum mai suna Nehemiah Sunday Udo mai shekaru 65, daga garin Ekpene Obo a karamar hukumar Esit Eket, ya na mallakar makami.”
Ta bayyana cewa “an kama wanda ake zargin a kan hanyar Ibeno Beach kuma aka kai shi fadar dagacin garin,” tana mai cewa “an tura tawagar sintiri cikin gaggawa zuwa wurin, inda aka kama wanda ake zargin tare da abubuwan da aka samu a hannun sa, sannan aka kai su Hedikwatar Rundunar don ci gaba da bincike.”
Ta lissafa abubuwan da aka samu tare da shi da suka haɗa da bindiga mai baki biyu, da harsashe guda daya, da fitilar hannu guda daya, da kuma jakar matafiya dauke da kayan sakawa.
“A yayin bincike, wanda ake zargin ya bayyana cewa shi mamba ne na ƙungiyar mafarauta ta ƙasa,” in ji ta, tana mai tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike don gano asalin aikin sa da manufar sa a yankin.
A wani lamari na daban, DSP John ta bayyana cewa “a ranar 21 ga watan Fabrairu 2025, da misalin ƙarfe 8:10 na dare, jami’an ‘yan sanda dake kan gudanar da sintiri da bincike a kan hanyar Ikot Udoma karamar hukumar mulkin Eket, in da suka kama wani mutum mai suna Emmanuel Sylvanus Ekan, dauke da bindiga ƙirar gida.”
Ta ƙara da cewa “an gaggauta kama shi, kuma an tsare shi don ci gaba da bincike.”
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar CP Baba Azare, ya bayyana cewa rundunar ba za ta lamunci aikata laifukka ba, yana mai jaddada aniyar rundunar na tabbatar da tsaron al’umma da kiyaye doka da oda, ya kuma yi kira ga jama’a da su rika bayar da rahoton duk wani mutum mai ɗabi’ar da ba ta dace ba ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa domin daukar matakin gaggawa.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
An banka wa gidaje 24 da runbunan ajiyar hatsi wuta a jihar Jigawa bayan wani rikici ya ɓarke tsakanin Hausawa da Fulani.
-
Sojoji sun isa wasu ƙauyuka biyar a jihar Kebbi dan farwa Lakurawa, bayan sun kai harin da ya yi ajalin mutum 10.
-
Gwamantin Edo ta rushe gidan wani mutum saboda zarginsa da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.
-
Gwamantin Kano ta ƙulla yarjejeniyar samar da sabbin motocin sufuri na zamani masu amfani da CNG.
-
Jam’iyyar PDP ta yi Alla wadai da dakatar da Sanata Natasha.