Ɗan China Ya Yiwa Ƴar Najeriya Kisan Gilla.

Page Visited: 5594
3 2
Read Time:1 Minute, 5 Second

Daga Ummahani Ahmad Usman

Rahotanni daga jihar Kano, a Arewa maso Yammacin Najeriya, na cewa hukumomi a Kano sun cafke wani dan kasar China mai suna Mr Geng bisa zargin hallata wata mata Ummukulsum Buhari, da aka fi sani da Ummita a unguwar Janbulo.

Freedom Radio ta cewa , Mr. Geng wanda tsohon saurayin Ummulkhairi ne ya kutsa kai cikin gidansu a daren Jumu’a , inda ya caka mata wuka, bayan afkuwar an garzaya da ita asibitin UMC da ke Janbulo , a nan ne kuma rai ya yi halinsa.

Freedom Radio ta ce, wani makusancin marigayiyar ya ce , sun shafe kusan shekaru biyu suna soyayya da Mr Geng kafin ta yi aure da wani.

Sai dai daga bisani auren nata ya mutu , amma shi Mr Geng bai daina bibiyarta ba.

Tuni dai jami’an hukumar shige da fice ta kasa suka cafke Mr Geng tare da mika shi ga yan sanda domin ci gaba da bincike.

‘Yan Sanda Na Bincike Kan ‘Dan Sandan Da Bindigar Sa Ta Tashi Ta Bindige Abokin Aikinsa A Jihar Kano.

Kano: Rundunar Yan Sanda Ta Kama Wani Da Ake Zargin Barawon Mota Ne.

Kano: Rundunar Yan Sanda Ta Kama Yan Daba Yayin Da Suke Tsaka Da Saran Junansu

Freedom Radio ta so jin ta bakin mahaifiyar Ummita amma bata amince ta yi magana ba.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Matashi Ya Yiwa Mahaifin Budurwarsa Mummunan Rauni Bayan Ya Hana Shi Kaiwa Dare Idan Yaje Zance.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Saurayin ya yiwa mahaifin budurwarsa rauni ne bayan da baban budurwar tasa ya hana shi kaiwa dare idan yaje zance a garin Ɗan Hassan, da ke ƙaramar hukumar Kura ta jihar Kano da ke arewacin Najeriya. Arewa Radio ta rawaito cewa, an jiwa mahaifin budurwar raunine bayan da ya umarce saurayin […]

Read More
Labarai

Sojoji sun sake yin juyin mulki a kasar Burkina Faso.

Sojoji a Burkina Faso sun hamɓarar da shugaban gwamnatin sojan ƙasar, Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba a yau Juma’a, bayan ya hau mulki a watan Janairun da ya gabata. Wata sanarwa da sojojin suka karanta ta kafar talabijin ɗin ƙasar ta ce an rufe dukkan iyakokin ƙasar na ƙasa daga daren yau. Haka nan sun […]

Read More
Labarai

Lauyan Gwamnatin Kano Ya Nemi Kotu Ta Yiwa Abduljabbar Hukunci.

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci dake Kofar Kudu Karkashin me Shari’a Ibrahim Sarki Yola ta ce za ta ayyana ranar da za ta yanke hukunci kan karar da Gwamnatin Jahar Kano ta shigar da Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara bisa zarginsa da kalaman batanci. Yayin zaman na Yau dukkannin bangarorin Shari’ar sun gabatar da Jawabansu na karshe […]

Read More