June 8, 2023

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Ɗan Takarar Gwamnan Kano Da Ya Sha Kayi Ibrahim Khalil Ya Ce Yanzu Ya Fara Takarar Gwamna A Jihar.

Page Visited: 190
0 0
Read Time:1 Minute, 8 Second

Daga Umar R Inuwa

Malam Ibrahim Khalil, wanda shine ya yi wa jam’iyyar ADC takarar gwamnan jihar Kano a zaben 18 g watan Maris ya ce yanzu ya fara yin takarar gwamnan jihar Kano la’akari da irin kyawawan manufofin sa ga jihar.

Ibrahim Khalil ya ya bayyana hakanne a wani shiri na musamman da aka yi da shi a wani gidan radiyon Guarantee Radio da yammacin ranar talata.

A cewar sa duk da kura-kuran da suke ganin an tafka a zaben da aka gabatar a Asabar ɗin ƙarshen makon nan, ba za su je kotu ba.

Yana mai cewa, tun daga yanzu har zuwa lokacin kakar Zaɓe na gaba za su kasance cikin wayarwa da mutane Kai bisa tafiyarsu ta.

Khalil, ya kuma taya Abba Kabir Yusuf murna bisa ayyanashi da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa ta yi a matsayin wanda ya lashe zaɓen daya gudana, tare da yimasa addu’ar Allah ya bashi ikon sauke nauyin daya ɗauka.

Hukumar zaɓe INEC ta sanar da Abba Kabiru Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya kashe zaɓen gwamnan Kano da ƙuri’a 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna ya samu ƙuri’u 890,705.

Sakamakon ya nuna cewa jam’iyyar PDP ce ta zo ta uku Sadik Wali ya samu ƙuri’u 15,957, sai shi Ibrahim Khalil da ya na jam’iyyar ADC da ya samu ƙuri’a 12,832.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *