Ɗan Turkiyya: Yana Iƙrarin Kashe Kansa, Ya Cakawa Kansa Wuƙa Sai Naji Tsoro A  Nima Kada Ya zo Ya Cutar Dani.- Ƴar Kano.

Page Visited: 1283
1 0
Read Time:2 Minute, 27 Second

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Rundunar ƴan sandan Kano ta tabbatar da samun ƙorafi daga wata budurwa da aka sakaya sunanta kan wani saraurayinta ɗan ƙasar Turkiyya da ke bibiyarta bayan sun shafe watanni uku suna tare.

“Mun samu ƙorafi daga wannan matashiya kan ta kawo kanta nan shelkwatar yan sanda da ke nan Bomfai tana neman ɗauki da agaji akan wani ɗan ƙasar Turkiyya wanda ta shigar da ƙorafi a kansa,” a cewar rundunar.

Kakakin rudunar ƴan sandan jihar Kano Sifiritandan yan sanda Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da hakan ga nema labarai a ranar Laraba.

A cewar Kiyawa kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Abubakar Lawan ya bayar da umarnin yin “binciken ƙwaƙwaf a kan wannan lamari.”

Budurwar Ta Kai Kanta Ga Ƴan Sanda Ne Bayan Saurayin Ta Ɗan Ƙasar Turkiyya Na Neman Ta Ruwa A Jallo.

Kotu Ta Umarci ASUU Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Ke Yi Tsawon Watanni 7.

Budurwar Ta Kai Kanta Ga Ƴan Sanda Ne Bayan Saurayin Ta Ɗan Ƙasar Turkiyya Na Neman Ta Ruwa A Jallo.

Mashiyar wadda ba a bayyana sunanta ba ta ce ta shiga tsorone bayan da ta samu labarin kiran da ake zargin wani ɗan ƙasar China ya yiwa wata tsohuwar budurwarsa a jihar Kano, al’amarin dake gaban kotu.

“Wani al’amarine ya ke faruwa dani wanda hankalina ya tashi sosai naga ya dace nazo hukumar ƴan sanda na sanar da wannan al’amarin da yake faruwa.”

“Wani ɗan Turkiyya ne ya ke sona ni kuma bana son shi, lamarin ya kai yana ta bibiyata yana bin mutanen da suke mu’amala dani har yana iƙrarin kashe kansa, ya cakawa kansa wuƙa sai naji tsoro a kan nima kada ya zo ya cutar dani,” in ji budurwar.

Ta kuma ƙara da cewar a halin yanzu tana son hukuma ta shiga tsakaninsu “da farko ban yi tunanin haka ba, sai da naga wannan abin da ya faru a kan ɗan Chinan nan da yarinyar nan sai naji hankalina ya tashi sosai.”

“Wannan dalilin ne yasa nazo hukumar ƴan sanda domin ta shiga tsakanina da shi,” a cewar ta.

Matashiyar ta cigaba da bada labarin yadda ya cakawa kansa wuƙa “ya caka ma kansa wuƙa ne kuma nima yana ta bina bayan na gaya mai bana son sa bana son alaƙa da shi, to amma yaƙi ya dena, har ya kai yana bibiyata yana matsawa rayuwata.”

“Mun kai tsawon wata uku da shi na zo nayi soyayya da shi ba, in yi tinani a kan rayuwata, to ban san me yake da niyar yi ba, shi yasa nazo dan hukuma ta shiga tsakanina da shi,” kamar yadda ta matashiyar ta bayyana.

Budurwar ta shigar da ƙorafi ne kwanaki biyar da wani ɗan ƙasar China ya yiwa wata tsohuwar budurwarsa a jihar Kano kisan gilla, al’amarin da ya ta da hankalin al’ummar jihar Kano dama wasu yan Najeriya.

Tini dai wata kotu a jihar Kano ta aike da ɗan Chinan da ake zargin gidan Kurkuku.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Matashi Ya Yiwa Mahaifin Budurwarsa Mummunan Rauni Bayan Ya Hana Shi Kaiwa Dare Idan Yaje Zance.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Saurayin ya yiwa mahaifin budurwarsa rauni ne bayan da baban budurwar tasa ya hana shi kaiwa dare idan yaje zance a garin Ɗan Hassan, da ke ƙaramar hukumar Kura ta jihar Kano da ke arewacin Najeriya. Arewa Radio ta rawaito cewa, an jiwa mahaifin budurwar raunine bayan da ya umarce saurayin […]

Read More
Labarai

Sojoji sun sake yin juyin mulki a kasar Burkina Faso.

Sojoji a Burkina Faso sun hamɓarar da shugaban gwamnatin sojan ƙasar, Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba a yau Juma’a, bayan ya hau mulki a watan Janairun da ya gabata. Wata sanarwa da sojojin suka karanta ta kafar talabijin ɗin ƙasar ta ce an rufe dukkan iyakokin ƙasar na ƙasa daga daren yau. Haka nan sun […]

Read More
Labarai

Lauyan Gwamnatin Kano Ya Nemi Kotu Ta Yiwa Abduljabbar Hukunci.

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci dake Kofar Kudu Karkashin me Shari’a Ibrahim Sarki Yola ta ce za ta ayyana ranar da za ta yanke hukunci kan karar da Gwamnatin Jahar Kano ta shigar da Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara bisa zarginsa da kalaman batanci. Yayin zaman na Yau dukkannin bangarorin Shari’ar sun gabatar da Jawabansu na karshe […]

Read More