Ɗariƙar Ƙadiriya Ta Sanar Da Taron Ta Na Maukibi Da Kuma Wasu Manyan Taruka Da Suke Yi Duk Shekara.

Page Visited: 1728
0 0
Read Time:1 Minute, 35 Second

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Ɗariƙar Ƙadiriya ta sanar da cewa za ta yi taron Maukibi na wannan shekara a ranar Asabar 5 ga watan Nuwamba na shekarar 2022.

Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Nalam Nura Abba Maimuƙami, shugaban Ƙadiriyya Soshiyal Midiya, ya wallafa a shafinsa na Facebook, a ranar  Alhamis din nan.

Sanarwar ta ce shugaban Ɗariƙar Ƙadiriya a Najeriya da Afrika Sheikh Qaribullahi Nasir Kabara, ne ya bayar da sanarwar.

“Tsarin jadawalin tarukan mauludin Annabi SAW, wanda aka amince za a yi.”

Shehin ɗariƙar Ƙadiriya zai dawo Kano daga wata ziyara da ya ke yi a ƙasar Morocco a ranar 19 ga watan Satumba, inda kuma zai yi tafiya zuwa  jihar Sokoto a ranar 24 ga watan na Satumba wanda zai je domin yin mauludi Sheikh Usman Ɗan Fodiyo,” in ji sanarwar.

Sheikh Kabara ya ƙara da cewa zai jagoranci taron mauludin Annabi SAW a unguwar Kabara a ranar 29 ga watan na Satumba a wannan shekara da nuke ciki, wanda kuma daga nan zai jagoranci wani mauludin Annabin a ranar 7 ga shi watan Oktoban a fadar mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.

“Zan kuma kara yin wani mauludin a ranar 15 ga watan Oktoba a birnin Abekuta na jihar Ogun, daga nan zan sake yin zuwa wani mauludin Annabin da za a yi shi Al’Isobatul Qadiriya da ke Agegen jihar Lagos,” inji malamin.

A karshe sanarwar ta ce “za a yi taron Maukibin Ƙadiriyya a ranar biyar ga watan Nuwamba na shekarar 2022.”

Gwamnatin Kano Ta Yiwa Sheikh Qaribullahi Kabara Kyautar Fili.

Kuskure Ne Rufe Titi A Yayin Sallar Juma’a, Cewar Sheikh Qaribullahi Nasiru Kabara.

Rashin Tsaro: Babu Aminci Na Zaman Lafiya, kwanciyar Hankali Ya Zama Rayukan Al’umma Suna Cikin Barazana,-Kabara.

Taron Maukibi dai, mabiya ɗariƙar Ƙadiriya na yin sane a duk shekara domin murnar zagayowar ranar da aka haifi babban shehin Ɗariƙar Sheikh Abdulƙadir Jilani.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Matashi Ya Yiwa Mahaifin Budurwarsa Mummunan Rauni Bayan Ya Hana Shi Kaiwa Dare Idan Yaje Zance.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Saurayin ya yiwa mahaifin budurwarsa rauni ne bayan da baban budurwar tasa ya hana shi kaiwa dare idan yaje zance a garin Ɗan Hassan, da ke ƙaramar hukumar Kura ta jihar Kano da ke arewacin Najeriya. Arewa Radio ta rawaito cewa, an jiwa mahaifin budurwar raunine bayan da ya umarce saurayin […]

Read More
Labarai

Sojoji sun sake yin juyin mulki a kasar Burkina Faso.

Sojoji a Burkina Faso sun hamɓarar da shugaban gwamnatin sojan ƙasar, Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba a yau Juma’a, bayan ya hau mulki a watan Janairun da ya gabata. Wata sanarwa da sojojin suka karanta ta kafar talabijin ɗin ƙasar ta ce an rufe dukkan iyakokin ƙasar na ƙasa daga daren yau. Haka nan sun […]

Read More
Labarai

Lauyan Gwamnatin Kano Ya Nemi Kotu Ta Yiwa Abduljabbar Hukunci.

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci dake Kofar Kudu Karkashin me Shari’a Ibrahim Sarki Yola ta ce za ta ayyana ranar da za ta yanke hukunci kan karar da Gwamnatin Jahar Kano ta shigar da Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara bisa zarginsa da kalaman batanci. Yayin zaman na Yau dukkannin bangarorin Shari’ar sun gabatar da Jawabansu na karshe […]

Read More