September 22, 2021

A koma ga Allah da neman tuba, don kawo karshen Garkuwa da Mutane: Alh Salisu Garba. 

Page Visited: 197
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:1 Minute, 23 Second

Daga: Mu’azu Abubakar Albarkawa Kaduna

 

An bukaci iyayen yara dasu mai da hankalin su wajen kai yaran su makarantun islamiyya, don samun ilimin addini.

 

Alh. Garba Salisu Muhammad, wani mai kishin al-umma a karamar hukumar Zariya,shine ya shawarci iyayen yaran a lokacin gudanar da walima na dalibai da suka sami haddar Al-kur’ani mai girma a makarantar Mu’azu Bin Jabal litahafizul Kur’an dake Bayan Silma Tudun Wada zariya.

 

Yace, duba da halin da kasa ke ciki na garkuwa da mutane da sauran aikin bata gari, ya zama wajibi Jama’a su koma ga Allah ta hanyar tuba da neman gafarar Allah S. W. A inda yace hakan ba zai samu ba sai an sanya yara a makaranta sun sami ilimi addini.

 

Alh. Salisu Garba, ya yaba da irin kokarin da malaman ke bayarwa wajen mai da hankalin don baiwa yaran ilimin addini. Inda yayi kira ga iyaye da su kula da biyan kudin makarantar yaran nasu, don samun ilimin da ya dace.

 

Tun farko da yake nasa jawabin, Shugaban Makarantar Malam Aminu Abdullahi Assalafi, ya godewa mahalarta taron, inda ya bayyana cewa wannan shine karo na farko da suka yaye mahaddata.

 

Yace, sun sami nasara sosai daga kafa makarantar izuwa wannan lokaci, sai dai kalubalen da suke fuskanta yafi yawa.

 

Shugaban Makarantar, yace suna fuskantan kalubalen muhali na dun dun dun, don cigaban karatun daliban.

 

Wasu daga cikin daliban sun godewa malaman nasu, na irin kokarin da suka yi wajen Basu ilimi har suka kai ga wannan matsayin.

 

Taron ya sami halartan shuwagabannin al-umma da ‘yan siyasa da Jama’ar Anguwa, iyayen  yara da sauran su.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us