Deprecated: Unparenthesized `a ? b : c ? d : e` is deprecated. Use either `(a ? b : c) ? d : e` or `a ? b : (c ? d : e)` in /home/martabaf/public_html/wp-content/plugins/wp-socializer/core/templates/floating-sharebar.php on line 180
Abotar Pantami da FFK - Martaba FM
October 20, 2021

Abotar Pantami da FFK

Page Visited: 157
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:3 Minute, 18 Second

Daga Sulaiman Maijama’a

 

Ziyarar da shahararren makiyin addinin Musulumci, Makiyin Arewa da kuma Hausawa wato Femi Fani-Kayode ya kai wa Ministan Sadarwa da tattalin arziki Isah Ali Pantami, ya jawo cece-kuce tsakanin jama’a. BBC Hausa ta rawaito cewa Pantamin shi da kansa ya gayyaci FFK tare da Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle zuwa gidansa a daren ranar Juma’a, inda suka ci abincin dare, sannan suka tattauna al’amuranda suka Shafi kasa dama Duniya, har zuwa safiyar ranar Asabar.

Cikin “comments” sama da dubu karkashin rahoton BBC Hausa, a k’alla kashi casa’in na mutane na Allah wadai da wannan zayara. Wannan kuwa baya rasa nasaba da sanin kowa ne shi dai FFK k’iyayyar sa a fili yake ga duk wani abinda ya shafi Arewa, Ko Musulumci, ko Bahaushe; kalamansa sun munana.

Ko a watan Afrilun wannan shekara, FFk yayi munanan kalamai kan Pantami, inda ya kirashi da “Dan ta’adda, Mai tsattsauran ra’ayin addini, Mai ingiza mabiyansa.” FFK yace “Kamata yayi a Sanya wa Pantami sark’a a gark’ameshi a gidan kaso don Ko a titi bai dace a barshi yana tafiya ba balle zama a kujerar Minista.”

Kwatsam a kwanakin baya sai aka gano FFK tare da Ministan suna kashe hotuna cikin raha, a wajen daurin auren D’an shugaba Buhari. Sannan Kuma satin da ya wuce daridar Daily Trust ta wallafa FFK na cewa “babu Ministan da ya karya k’ashin y’an ta’adda kamar Pantami.”

Abinda masu tsokaci ke tambaya shine: ta yaya dukda munanan kalamai da yayi akan Ministan, kuma dukda kasancewar ministan babban malamin addinin Musulumci, amma zai gayyato FFK har gida, agansu suna dariya?

Ni a karamin fahimta na, ai kasancewar Pantamin malamin musulumci shi yasa ya nuna masa d’abiun addinin mu. Idan muka duba tarihin Annanbinmu Muhammad (SAW), akwai kafirai da yawa da suke tsananin gaba dashi, suka cutar dashi, suka cutar da musulumci da musulmai; amma hakan baisa Annanbinmu ya yi gaba dasu; Kullum sai dai yayi musu goma na arzik’i, hakan yasa da yawansu suka fahimci addinin Musulumci addinin karamci ne, suka shigo ciki.

Ya tabbata a tarihi, Abu-Sufyan Yana daga cikin mutanenda suka wahalar da Annanbinmu (SAW). Yayi duk mai yiwuwa don ganin addinin Musulumci bai Karbu ba. An dauki tsawon lokaci yana k’iyayya ga musulumci. Da akazo yak’in “hunain” Abu-Sufyan yazo yak’ar annabin mu sai akayi nasarar kamoshi cikin fursinonin yak’i aka kawo shi gaban Annanbinmu. A tsammanin sa yau k’arshensa yazo amma abin mamaki, karamci irin na annabi Muhammad (SAW) ya tara masa dukiya mai yawa, ya Kuma bashi zaratan sojoji suka rakashi, Annanbinmu yace Kaje mun yafe maka. Abu-Sufyan zuciyarsa ta cika da mamaki. Ace duk sharrin da yayi wa musulumci, Yau yazo yak’ar Annanbi an kamoshi ace kuma an masa wannan karamci?

Sannan Kuma daga baya da akazo”Fat-hu Makkah, Manzon Allah (SAW) ya sake masa Wani karamci: kafirai sun tsorata sunata guduwa, Sai Annanbinmu ( SAW) Yace: duk Wanda Ya shiga. gidan Abu-Sufyan ya tsira. Wannan kyawawan dabi’u da Yasa Abu-Sufyan yazo ya karb’i addinin Musulumci, Sai mutane sukayita zuwa Suna shiga musulumci.

Banda wannan, akwai wata mak’wabciyar Annanbinmu wanda saboda k’iyayya gareshi Kullum Shara take zuba masa cikin gida. Sai wani lokaci aka kwana biyu Annanbi (SAW) baiga an zubo sharan ba. Da ya tambaya sai akace ai matar batada lafiya ne. Annanbinmu sai yaje ya gaisheta. Wannan mata dalilin haka ta karb’i musulumci.

Mufa a musulumci Zuma muke dashi, Ko an bamu mad’aci mu Zuma muke bayarwa, in an mana Sharri da alkhairi muke sakawa, in an k’imu mu so mutum. Wannan shine abinda musulumci Ya koyar damu.

Pantami a matsayinsa na malamin addinin Musulumci ya san duk wad’annan k’issoshi da na kawo, dama wasu da ban kawoba, ya karantasu a littafin kuma ya karantar damu almajirai.

Saboda haka Idan ka tambayeni meyasa Pantami ya gayyaci mak’iyin musulumci zuwa gidansa Kuma ya masa karamci; sai ince maka
Yayi koyi ne da Annanbinmu Muhammad (SAW).

Mafhoom? Wassalam🙏

Maijama’a, Faculty of Communication, BUK
sulaimanmaija@gmail.com

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us