Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Shahararren ɗan bindigar nan ya addabi jihar Zamfara da Katsina da wasu sassan Arewa maso Yammacin Najeriya Ado Alero Ƴandoto, wanda kuma aka naɗa sabon Sarkin Fulanin Ƴandoton jihar Zamfara ya ce ban sai adadin ƴan bangar daya kashe ba.
Ado Alero ya bayyana hakanne cikin wani rahoto binciken ƙwaƙwaf na tawagar ‘BBC Africa Eye’ wanda aka ra saki ranar Litinin.
“Ai ni ban taɓa ɗauko mutum ba, sai dai yara, amma ni da kaina ban taba dauko mutum ba sai dai in harbe shi,” in ji Alero.
Game da zargin kisa kuwa Ado Alero, ya ce shi zuwa yanzu bai san adadin mutanen daya kashe ba.
“Gaskiya tsakani da Allah, gaskiya ban san iyakar su ba.”
Ya kuma alaƙanta kashe-kashen da suke yi da wata hanyar da zasu nunawa gwamnati wani abu da ke faruwa domin acewar su basu san yadda ake zanga-zanga ba.
“To zanga-zangar mu ai ya bindiga ce, don kaga bamu san inda zamu ga ɗan jarida ba, zanga-zangar mu in ka ganmu mun dakko bindigoginmu ne mu je karkara ita ce zanga-zangar mu gaskiya.” “Lokacin gwamnati zata tashi ta gano cewa shin mene matsalar mu, idan ta neme mu, mu gaya mata matsalar mu.”
A makon jiya ne aka naɗa Ado Alero, sarautar Sarkin Fulanin Ƴandoton Daji da ke jihar Zamfara, naɗin da ya bar baya da kura.
Nafi Son Kashe Mutane Maimakon Garkuwa Da Su, -Ado Alero.
Uku Daga Cikin Fasinjojin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna Sun Kuɓuta.
Daga Yanzu Duk Wani Ɗan Zamfara Zai Iya Mallakar Bindiga Domin Ya Kare Kansa.
Tini dai gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da Sarkin ‘Yandoton Daji da ke yankin karamar hukumar Tsafe ta jihar, sakamakon naɗin da ya yi.
Ana zargin Ado Alero ne ya jagoranci tawagar yaransa suka kai harin da ya yi sanadiyyar kashe gwamman mutane da kone gidaje da shaguna a kauyen Kadisau na karamar hukumar Faskari jihar Katsina a shekarar 2019, wanda kuma aka sa kyautar miliyan biyar ga duk wanda ya kai Alero ga jami’an tsaro ko kuma ya kai labarin inda yake.
To sai dai a wata hira da DW Hausa Ado Alero ya musanta cewar da hannunsa a kai harin na garin Kadisau.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Har yanzu ina matuƙar son Buhari, in ji fasinjan da ya kuɓuta daga hannun ƴan bindiga.
-
Kotu Ta Yi Fatali Da Buƙatar Abdujabbar Kan Neman Sauya Masa Kutu.
-
Kano: Matashiya Yar Shekara 16 Ta Rataye Kanta A Daki.
-
Sojojin Najeriya Na Farauta Waɗanda Suka Hausawa A Jihar Imo.
-
Gwamnan Kogi Ya Hana Sanya Takunkumin Rufe Fuska.