December 2, 2021

Ado Da Kwalliya 2

Page Visited: 387
1 0

Notice: Trying to access array offset on value of type bool in /home/martabaf/public_html/wp-content/plugins/social-media-share-buttons/mozedia-sharing.php on line 283
Read Time:1 Minute, 44 Second

Daga Zainab Muhammad

 

Barkanmu da sake hadewa a wannan fili na kwalliya Ado da Kwalliya Daga Nan Martaba FM Online.

A yau mun taho muku da tsaraba Mai kyau, domin kuwa zaku ga yadda ake hanyoyi wanda ake bi don samun fata Mai kyau Kuma me haske, har wa yau za kuma mu nuna muku hanyoyi da za’a bi don gyara fatar jiki ba tare da an kashe kudi Mai yawa ba.

Yana da kyau koyi dabaru da Masu yawa wanda zasu taimaka wajen inganta fatar jikin mu dama Lafiyar mu baki daya.

Ga misali idan kin/ka saba da sayan kayan kwalliya, to wannan hadin da zaku koya zai taimaka a ranar da babu, ma’ana za’a iya hada guda Daga Cikin wanan dabarun da zamu zayyano su bi da bi.

A sha karatu lafiya….

GYARAN JIKI NA DILKA:

Dilka Yana daya Daga Cikin abubuwa Masu kyau na Gyran Jiki saboda Yana dauke da Wasu organic supliments da suke Kare fata Daga tsagewa ko bushewa.

Idan za’ayi irin wannan Gyra, za’a buƙaci

  1. Garin Dilka
  2. Kurkum
  3. Man Zaitun
  4. Kwai

Yadda za’a haɗa shi kuwa za’a dibi garin Dilka cokali 3-4 a zuba a mazubi ko Kuma iya yawan abunda ze ishi jiki, sannan sai a zuba masa ruwa Mai zafi ko ruwan dumi.

Jimawa kadan idan aka taba za’a ga yayi laushi, sannan sai a kawo garin kurkum a zuba a Cikin hadin.

Za’a Samu man zaitun kamar cokali 1 ko 2, sai a fasa kwai guda 1 a ciki, sannan a dan kara ruwa dan dai-dai sai a kwaba shi da kyau.

Za’a shafe fuska da shi har zuwa jiki, sai abar shi ya bushe na tsawon mintuna 15 ko 20 .

Idan ya bushe za’a murje da kyau, Kuma Daga Nan ma za’a ga jiki ya Fara haske saboda ya dago fatar daya lalace ko mataccen fata.

Shikenan dama an surka ruwan dumi sai a shiga wanka Amma please Kar a murje jikin sosai da soso saboda an murje shi Kafin a shiga wanka da Dilka.

Ku kasance da Martaba FM Online.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *