Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Ƙasar Amurka da Wales sun tashi 1 da 1 a wasan farko da suka buga cikin rukunin B na gasar cin kofin duniya na 2022.
Wannan dai shine wasa na biyar da aka buga a wasan a baki ɗaya cikin gasar da aka fara ranar Lahadin da ta gabata kuma wasa na biyu a rukunin B.
Amurka ce ta fara sa kwallo a ragar Wales a minti na 36 da take wasan ta hannun ɗan wasanta T.Weah, haka aka tafi hutun rabin lokaci Wales na nema.
To amma bayan dawowa daga hutun a minti na 82 G.Bale ɗan wasan Wales ya farke kwallon.
Ecuador Ta Zargawa Qatar Mai Masaukin Baki Kwallo 2 A Raga.
Worldcup 2022: Ingila Ta Lallasa Iran Da Ci 6 Da 2.
Senegal Ta Yi Rashin Nasara A Hannun Netherlands A Gasar Cin Kofin Duniya.
Wannan kunnen doki da su ka yi ne yasa suka raba maki ɗai-ɗai tsakaninsu, inda ƙasar Ingila ke jan ragamar teburin da maki uku Amurka ke bi mata baya da maki ɗaya sai Wales da ke ta uku da maki ɗaya in kuma Qata ke ta ƙarshe bayan ta yi rashin nasara a wasanta na farko.
A ranar 25 g watan Nuwamba Amurka za ta buga wasanta na biyu da ƙasar Ingila, inda ita kuwa Wales za ta ɓarje gumi da Iran wadda ta kwashi kashinta a hannun Ingila bayan cinta 6 da biyu.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
An Buƙaci Kutu Ta Tsawaita Mulkin Buhari Da Kuma Ƙara Wa’adin Rantsar Da Tinubu.
-
2023: Ba Zan Bari A Yi Magudin Zaɓe Ba- Buhari.
-
Morocco Ta Sallami Spain daga Gasar Kofin Duniya.
-
Faransa Mai Ɗauke Da Kofin Duniya Za Ta Fara Kare Kofinta A Yau Talata
-
A Halin Yanzu Tunisiya Ce Ta Ɗaya A Rukunin D Bayan Ta Yi Canjaras Da Denmark A Cigaba Da Gasar Cin Kofin Duniya.