June 27, 2022

An bayyana amfani da audugar mata a matsayin hanyar kariya daga cututtuka

Page Visited: 471
0 0
Read Time:1 Minute, 11 Second

Daga Jibrin Hussain Kundum

 

Wata gidauniyar tallafawa kananan yara mai suna Child Hope Foundation a turance ta raba kayayyakin kula da kiwon lafiya wa mata da ke kauyen Dungal a karamar hukumar Bauchi a wani mataki na taimaka musu musamman a lokacin jinin al’ada.

Shugaban kungiyar a jihar Bauchi Comrade Usman Jibrin Arab shi ne ya jagoranci rabon kayan hadi da taron wayar da kan al’umma da ya gudana a kauyen na Dungal.

Ya bayyana cewa manufar shirya taron shine a ilimantar da iyaye mata dangane da amfani da audugar a yayin da suke jinin al’ada, wanda bisa cewarsa hakan zai taimaka matuka wajen kare su daga cututtuka a lokacin da suke al’ada.

Usman Arab ya nanata bukatar da ke akwai na iyaye mata su maida hankali wajen kula da tsaftar jikinsu don samun rayuwa cike da koshin lafiya.

Da take jawabi a wajen taron, Wata daliba a kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma na Asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi Amina Abubakar Sadiq ta bayyana muhimmancin amfani da audugar mata a lokacin da matan ke al’ada.

Sai tayi kira ga mahalarta taron da suyi amfani da ilimin da suka samu wajen taron don kwalliya ta biya kudin sabulu.

A nasa bangaren sakataren gidauniyar ta “CHILD HOPE FOUNDATION” Comrade Rilwanu Ahmad Na’ibi kira yayi wa hukumomin gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu da su yi koyi da irin wannan karamci da gidauniyarsu tayi.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *