Ana fargabar wani ɗan sanda a ƙasar Guinea Bissau, ya rasa ransa bayan zargin yin harbe-habe a kusa da fadar shugaban ƙasar da ke Bissau babban birnin ƙasar.
Sai kuma babu wata hukumar da ta tabbatar da hakan, an dai ce sojoji sun kewaye ginin fadar shugaban kasar.
An kuma fahimci cewa Shugaba Umaro Sissoco Embaló yana cikin fadar.
Lamarin na faruwa ne a yayin da Shugaba Embaló da Firaiminista Nuno Gomes Nabiam suke gudanar da taro.
BBC Hausa ta rawaito cewa, wani mazaunin birnin ya shaida wa shirin BBC Focus on Africa na rediyo cewa an kashe wani dan sanda sakamakon harbe-harbe.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Rundunar Ƴan Sandan Jihar Kano Ta Gargadi Mazauna Jihar Kan Atisayen Harbin Bindiga A Kalebawa.
-
Ba Zamu Lamunci Daba Da Shaye-Shaye A Unguwarmu Ba- Al`Ummar Dala.
-
Ayyukan Laifin Da Aka Aikata A Kano Cikin Shekarar 2022 Sun Ragu Fiye Da 2021- Ƴan Sanda.
-
Jami’an Tsaro Sun Hallaka Ƴan Bidinga Tare Da Ragargaza Maɓoyarsu.
-
TSARO: Gwamnatin Buni ta na ci gaba da bai wa jami’an tsaro cikakken goyon baya don tunkarar matsalolin tsaro a Yobe