January 19, 2022

An Kalubalenci Shirin Abduljabbar Na Fito Da Wani Littafi Daya Kunshi Cin Zarafi Ga Addinin Islama.

Page Visited: 354
0 0
Read Time:1 Minute, 7 Second

Daga Suleman Ibrahim Moddibo

Limamin masllacin Juma’a na Kanzul Dudalsami, Sheikh Mustafa Sheikh Dr Nasiru kabara Alkali, ne ya kalubalanci Abduljabbar din bayan bayyanar wani faifan bidiyoe da Abduljabbar ke cewa yana rubuta wani littafi da yafi sallah muhimmanci.

Inda Alkali Malam Mustapha ya ce baza su yarda da fitar da littafin ba ” Ni wannan shine ra’ayina tun kafin littafin ya fito mu bayyana inkarinmu bamu yarda ba duniya ta sani duniya taji cewa be dena ba, kuma abunda ma aka tsare shi akai be fasa ba, cigaba ma yake yi ga shi nan yana ma zakulkulo wasu abubuwan”.

Alkali Mustapha, ya ce baza su fasa yi masa inkari ba tinda bai dena ba, “To duk da an hana shi din to muma bazamu dena yi masa inkari ba duk sanda yayi wata magana nan take ya ganmu a media ana yi masa in karinta ba tare da ko wani jinkiri ba”.

A dai cikin bidiyon da ya fara yawo a kafafen sada zumunta tun ranar 15-05-2021 cikinsa Abduljabbar yace anan gaba zai sake saka rana domin yin makamancin irin zaman da yayi a bidiyon, inda a cikin bidiyon ya cigaba da cewar, ” yanzu aikin wannan rubutu da nake ko sallah sai dai ta nuna masa hukuncin wajibci, ba mahimmanci ba, ita kanta sallar tana bukatar aikin da ake yi” a cewar sa.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *