January 31, 2023

An Koyar Da Gwamman Matasa Kiwon Tumaki A Jihar Bauchi.

Page Visited: 101
0 0
Read Time:50 Second

Daga Muhammad Sani Mu’azu
Kimanin matasa maza da mata 35 ne aka horar kan dabarun kiwon tumaki, don dogaro da kansu da kuma yaki da talauci.

Taron wanda kamfanin Ivie General Contractors da cibiyar kimiyyar dabbobi ta Najeriya ta shirya karkashin tsarinta na samar da abin yi wa marassa galihu a bangaren kiwon dabbobi a jihar Bauchi.

A ƙarshen shirin na wuni guda da ya gudana a Bauchi, kowanne mutum daya da ya ci gajiyar shirin ya samu rago daya da tinkiya a matsayin jari, haɗi da kanwar dabbobi.

A nasa jawabin, shugaban sashin horaswa na cibiyar Dakta Babatunde Fola Adebayo, ya ce sun zo Bauchi ne don samar da aikin yi wa matasa tare da koya musu yadda ake kiwon tumaki.

Acewarsa, mutane 35 ne suka ci gajiyar shirin da suka hada da maza da mata ne da aka zabosu daga sassa dabam dabam na jihar.

Babatunde ya jaddada cewa dabbobin da aka bayar sai da aka zabo masu kyau da zasu samar da alfanu wa manoman.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *