Deprecated: Unparenthesized `a ? b : c ? d : e` is deprecated. Use either `(a ? b : c) ? d : e` or `a ? b : (c ? d : e)` in /home/martabaf/public_html/wp-content/plugins/wp-socializer/core/templates/floating-sharebar.php on line 180
An Shiga Rudani A Garin Kankara Na Jihar Katsina Sakamakon Kwararar 'Yan Bindiga. - Martaba FM
October 20, 2021

An Shiga Rudani A Garin Kankara Na Jihar Katsina Sakamakon Kwararar ‘Yan Bindiga.

Page Visited: 124
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:50 Second

Mazauna karamar hukumar Kankara na jihar Katsina sun shiga rudani sakamakon kwararar ‘yan bindiga da ake zargi wadanda suka gudo ne daga Zamfara a sakamakon matsin lamba daga jami’an tsaro.

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ‘yan bindigar na tserewa ne daga dazukan Zamfara inda ake musu luguden wuta zuwa kauyukan Katsina.

Wani mazaunin kauyen Pawwa, ya shaidawa jaridar cewa ‘yan bindigar sun kafa shinge inda suke binciker mutanen da ke wucewa tsakanin titin Kankara zuwa Zango.

A cewar mutan yankin “Babban bukatar ‘yan bindigar yanzu shi ne samun abinci da man fetur, suna dauke da jarkoki, inda suke karbar wani adadi na mai daga masu ababen-hawa da kwace duk wani abinci da suka gani.”

Wannan na zuwa ne hayan karewar makwanni buyi da katse layukan sadarwa a jihar Zamfara, sai kuma cikin wata zantawarsa da BBC Hausa   

Gwamnan Zamfara Bello Muhammad, Matawallen Maradun, ya ce babu ranar bude layukan sadarwa a jiharsa.

“Dole mu tsawaita don burinmu tabbatar da tsaron al’ummarmu,” acewar gwamnan Zamfara.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us