An Yi Min Barazana Da Gargadin Daina Sukar Gwamnatin Kano,- Abba Hikima.

Page Visited: 145
0 0
Read Time:1 Minute, 36 Second

Daga Abba Hikima

Wani makusancin gwamnatin Kano ya shaida min cewa gwamnati Kano tana ganin rubutun da nake yi kuma bata jin dadin sa. Ya kuma roki/ yi min gargadi in daina. Har ya bani misalai da wasu abubuwa da suka faru ga makusanta na domin jan kunne gare ni amma ban ankare ba. To duk da cewa ni ba yaron kowa bane kuma yanci na na fadar albarkacin baki na a damfare yake da yanci na na rayuwa; Ma’ana in dai ina raye sai nayi magana, to zan daina sukar gwamnatin kuma zan ja hankalin sauran jama’a da su daina sukar gwamnatin amma a bisa sharadi daya;

Tunda mun fahimci sakon da muke aika wa na isar wa gwamnatin zamu koma yin kira ga ita gwamnatin a bisa abubuwan da muke ganin ya kamata ta yi.

Idan tayi wa al’umma wadannan ayyuka wallahi ba daina suka ba, yaba mata ma zamu yi, mama ba kin ta muke yi ba. Ayyukan ta muke ki.

Amma fa idan ba a gyara ba to su tabbata sun kara mana kaimin ci gaba da abun da muke yi wanda suke kallon sana suka.

Saboda haka zamu fara da kira ga gwamnatin Kano da ta kawo daukin gaggaawa wurin gyaran wasu tituna da magudanan ruwa a Kano, wannan babban matsala ce saboda naji yau ma BBC Hausa sunyi rahoto akai.

Gwamnan Kano Ganduje Ya Fara Aikin Titin Tudun Yola,- Abubakar Aminu.

Yajin Aikin Masu Adaidata Sahu Ƴan Sanda Sun Gurfanar Sama Da Mutum 60 Gaban Kotu.

Har Yanzu Matuƙa Adaidata Sahu Basu Janye Yajin Aikin Da Suka Tsunduma Ba.

Zan fara da titin Tudun Yola da na Darmanawa. Wadannan tituna sun yi matukar lalacewa kuma suna jawo hadari da asarar dukiya ga masu bin su.

Kuma kuyi comments da titunan da ya kama a gyara domin mu shaidawa gwamnatin, ku hada da hotuna domin karfafa hujja.

Muna rokon mai girma gwamna zai duba.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ra'ayi

Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Ga Wasu Zaɓaɓɓun Jihar Bauchi.

Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwaga; • Mai girma Gwamnar jihar Bauchi Sen. Bala Moh’d. • Sen. Lawan Yahaya Gumau (Sanata Bauchi ta kudu). • Sen. Halliru Sauda Jika (Sanata Bauchi ta Tsakiya). • Barr. Ibrahim Kashim (SSG Bauchi State Government). • Hon. Yakubu Shehu Abdullahi (Reps Bauchi LGA). • Hon. Abubakar Y Sulaiman (Speaker BAHA). • Hon. […]

Read More
Ra'ayi

Ya Kamata Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Sauya Tinani Kan Batun Cefanar Da Kadarorin Jihar,- Koli.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasar Najeriya jam’iyyar APGA Kwamared Abdullahi Muhammad Koli, ya buƙaci gwamnatin jihar Bauchi ta sauya tinani kan batun jinginar tare da cefanar da wasu kadarorin jihar. Koli ya buƙaci haka ne cikin wata zantawarsa da Martaba FM a birnin Bauchi. Ga wani sashin hirar tasa tare da […]

Read More
Ra'ayi

Mu Farka Matasa: Shin Ko Mun San Halin Da Muke Jefa Rayuwan Mu A Ciki Wannan Zamani?.

Daga Aliyu Muhammad Kabir A ko wani lokaci za kaji ana cewa matasa sune ‘kashin bayan kowace al-umma, amma ba zaka ta’ba ganin haka a zahiri ba, mune, shaye-shaye, sara suka, sata, bangan siyasa, da dai suran abubuwa marasa dadin ji. Mu dauki rayuwar manyan kasar mu, suma suna da yara matasa kaman mu, amma […]

Read More