Page Visited: 1626
Read Time:29 Second
Kimanin manyan kifaye wato “Whales” 230 ne suka makale a gabar tekun Tasmania ta yamma, kwanaki kadan bayan da aka gano wasu nau’in kifin “Sperm” guda 14 a gabar tekun wani tsibiri da ke arewa maso yammacin kasar Australia.
Ma’aikatar Albarkatun Kasa da Muhalli ta Tasmania ta fada yau Laraba cewa, tarin kifin da ke makale a bakin tekun Macquarie Harbor da alama wadanda ake kira “Pilot Whales” ne kuma a kalla rabin ana kyautata zaton suna raye.
Ma’aikatar ta ce wata tawaga daga shirin Marine Conservation Program tana hada kayan aikin zuwa ceto.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Shanun Sun Yi Zanga-zangar Ce Don Rashin Cika Alƙawuran Gwamnati A Indiya.
-
Budurwar Ta Kai Kanta Ga Ƴan Sanda Ne Bayan Saurayin Ta Ɗan Ƙasar Turkiyya Na Neman Ta Ruwa A Jallo.
-
Ango Da Amaryar Da Aƙali Ya Aike Su Gidan Ɗan Kande Bayan Zargin Azabtar Da Ɗan Kishiyarta.
-
Bauchi: Amarya Da Ango Za Su Ci Amarci A Gidan Yari
-
Kwamandan ’yan fashin daji zai auri daya daga cikin fasinjan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.