August 8, 2022

Ana Zargin Wasu Jami`an Gwamnatin Jihar Bauchi Da Kwacewa Mutane Babura Su Salwantar.

Page Visited: 299
0 0
Read Time:1 Minute, 10 Second

Daga Suleman Ibrahim Moddibo

Hukamar Rage Cinkoson Ababawan Hawa ta jihar Bauchi BAROTA na zargin wasu jami`n gwamnatin jihar Bauchi da kwacewa munate babura ba bisa ka`ida ba, su kuma batar.

Shugaban hukumar BAROTA Air Commodore Ahmad Tijjani Baba Gamawa Mai Ritaya, ne ya tabbatarwa Martaba FM zargin cikin wata zantawar sa da Suleman Ibrahim Moddibo a jihar Bauchi.

Baba Gamawa ya ce, “ yanzu haka maganar da nake maka akwai rahoto da muka samu kuma muna bincike, akan cewa wasu mutane sun saka rigar BAROTA sun je sun karbi mashinan mutane, wanda yake har yanzu ba`a ga inda mashin di suke ba, amma har yanzu muna bincike munsa `yan sanda su yi bincike, yayin da aka gama bincike muna tabbatar muku da cewa zamu tura su kotu”.

A saboda haka Baba Gamawa, ya bukaci mutane su kula sosai domin kada su fada hannun bata gari “ muna kira ga mutane indai bamu jami`an barota suka gani da motoci ba, kuma babu wata alama data nuna mune to kar mutne su yarda da su, suyi maza su kai rahoto ga jami`an tsaro mafi kusa da su”.

Tin farkon shekarar 2020 ne dai gwamnatin jihar ta hana acaba a jihar baki daya, acewar ta tayi hakan ne domin kare lafiya da dukiyoyin al`umma gami da rayukan su, said ai kuma har yanzu ana samun masu yin acaban nan da can a jihar.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *