ASUU: Dan Me Za A Ce Shugaban Kasa Ya Yi Watsi Da Ilimi? – Garba Doya.

Page Visited: 1467
0 0
Read Time:1 Minute, 6 Second

An yi kira ga gwamnatin na Najeriya karkashin shugababan kasa Muhammadu Buhari, ta kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jam`o`in Najeriya, ke yi tsawon wata shida.

Garba Doya Sarkin Yakin Ajiyan Bauchi, shugaban ko`odinetocin gwamnan jihar Bauchi, ne ya yi wannan kiran cikin wata tattaunawar kai tsaye da aka yi da shi a Martaba FM.

Garba Doya, ya ce “karatun ba gashi ana yi masa zagon kasa ba, yau ASUU watan su shida suna yajin aiki, dai dai ne ace ASUU sun yi wata shida gwamnatin tarayya ba ta yi wani abu ba, `ya`yan mu mun haifesu sun zama jahilai, dan me za a ce shugaban kasa ya yi watsi da ilimi? Yakamata abar komai a taimaki ilimi, duk duniyar data cigaba ta cigaba ne a kan ilimi, kuma ka tashi ma da kanka ka taimaki kanka ai ba zaka iya bas ai kana da ilimi, saboda yin karatu a gurin mu kamar sallar Azzahar ne, dole ne“.

ASUU Ta Yi Ƙarin Makonni 4 A Yajin Aikin Da Ta Ke Yi.

Zamu Rufe Tashoshin Jirgin Sama Dana Ƙasa Da Titunan Idan Ba’a Janye Yajin Aikin ASUU – Ɗalibai.

Ya kuma yi kira ga matasa a Najeriya musamman matasan jihar Bauchi su tashi su nemi na kansu ba tare da jiran aikin yid aga gwamnati ba.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ilimi

Ta Leƙo Ta Koma: Gwamnatin Najeriya Ta Janye Umarnin Da Ta Bayar Na Buɗe Jami’o’i.Q

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Gwamnatin tarayya ta janye umarnin da ta ba shuganannin jami’o’i na su koma bakin aiki. Tinda farko a safiyar ranar Litinin ɗin nan gwamnatin ta bawa shugabannin jami’o’in umarnin buɗe makaratun cikin wata wasiƙa mai lamba NUC/ES/138/Vol.64/135 da kungiyar NUC ta fitar. To sai dai ta yammacin ranar wata wasiƙar ta […]

Read More
Ilimi

Gwamnatin Najeriya Ta Umarci Shugabannin Jami’o’i Su Buɗe Makarantu.

Gwamnatin tarayya ta umarci shugabannin jami’o’i (VCs) da su sake bude makarantu tare da baiwa dalibai damar komawa karatu. Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun daraktan kudi da asusun kula da jami’o’in kasar, NUC, Sam Onazi, a madadin babban sakataren hukumar, Farfesa Abubakar Rasheed a Abuja a yau […]

Read More
Ilimi

Kotu Ta Umarci ASUU Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Ke Yi Tsawon Watanni 7.

Kotun ma’aikata ta sawa kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU birki kan yajin aikin da ta ke yi tsawon watanni. Da yake gabatar da hukunci kan bukatar wucin gadi da gwamnatin tarayya ta nema, Mai shari’ah Polycarp Hamman ya hana kungiyar ASUU ci gaba da yajin aiki har zuwa lokacin yanke hukunci kan shari’ar. Mai […]

Read More