May 18, 2022

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Atiku ya buɗe ayyuka a Bauchi

Page Visited: 697
0 0
Read Time:1 Minute, 15 Second

 

Tsohon mataimakin shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar Wazirin Adamawa ya ƙaddamar da bude ayyukan wasu muhimman hanyoyin doshe da Gwamna Bala Abdulƙadir Muhammad yayi.

Tun da misalin ƙarfe sha da ɗaya da ƴan daƙiƙai Alhaji Atiku Abubakar da tawagar sa suka sauƙa a filin tashi da sauƙar jirage na tunawa da marigayi Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa inda Gwamna Bala Muhammad, jami’an gwamnatinsa da kuma ɗumbim masoya suka tarbe su.

Da yake jawabi a fadar me martaba Sarkin Bauchi, Atiku, yace kalmomi ba za su misalta farin cikinsa kan tarba da ƙauna da jihar Bauchi ke nuna masa tsawon lokaci ba.

Ya yabawa Gwamna Bala Muhammad kan ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ke gudanawar wa tare da kira ga gwamnonin jam’iyyar APC da su yi koyi da Sanata Bala da sauran gwamnonin PDP wajen samar da ayyukan bunƙasa ƙasa.

Da yake buɗe hanyoyin doshe masu tsawon kilomita 4.4 da suka haɗa Ibrahim Baƙo-Ƙofar Gombe da Tirwun zuwa titin Maiduguri da aka sanya sunan sa, Wazirin Adamawa cewa yayi ayyukan na da rawar takawa kan haɓaka tattatilin arziki.

Ya ƙara da jinjina wa gwamnan da majalisar dokoki ta jiha kan haɗa don inganta ilimi, noma, lafiya da yaƙi da zaman kashe wando tsakanin matasa.

Tun farko da yake jawabi, Gwamna Bala Muhammad cewa yayi an sanya sunan tsohon mataimakin shugaban Najeriyar ne la’akari da kwazon sa wajen inganta ƙasa.

Yace cikin ƙasa da shekaru biyu gwamnatin sa ta kammala sama da hanyoyin sufuri talatin a birane da yankunan karkara.

 

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *