Atiku Ya Taya Musulmi Murnar Mauludin Annabi SAW Wanda Ya Siffanta Shi Da Mai Jin Ƙai.

Page Visited: 1803
1 0
Read Time:1 Minute, 8 Second

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Ɗan takarar shugaban Ƙasar Najeriya a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya taya al’ummar musulmi a Najeriya murnar zagayowar watan da aka haifi Annabi Muhammad S A W.

Atiku ya taya murnar ne a shafin sa na Facebook a ranar Talata.

“Jinkai, adalci, tausayi, son Zaman lafiya da Haɗin kai da Amana na daga cikin halayen fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) , Wanda ya koyar da mabiyan sa,” a cewar Atiku.

“Wadannan kyawawan Halaye ya nuna su a aikace kuma ya yi umarni da ayi su.”

“Yayin da al’ummar Musulmin duniya ke marhabin da watan Rabi’ul Auwwal, wato watan Maulidi, ina mika sakon murna da zagoyowar wannan Rana ga Musulmin Najeriya, in ji shi”

Al`ummar Jihar Kaduna Na Cigaba Da Bayyana Farin Cikin Su Da Ranar Mauludin Annabi

Atiku Ya Gana Da Sanatocin Jam’iyyar PDP.

Ya kuma yi kira ga Muslunci su zama masu koyi da Annabi S.A.W, “ina kira a gare mu da sauran ‘yan Najeriya da mu yi koyi da wadannan halayen na fiyayyen halitta shugaba Annabi Muhammad SAW, domin Dora kasar mu kan tafarkin ci gaba Mai dorewa.”

“Hakika yanzu lokaci ne mai mutukar mihimmanci da kasar mu ke bukatar hadin kai, kaunar juna da zaman lafiya.”

“Ina fatan zamu yi koyi da wadannan halayen na fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW domin dawo da martabar kasar mu.”

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Mayan Titunan Jihar Kano Da Gwamnati Ta Haramtawa Masu Adaidata Sahu Bi.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Gwamnatin jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya  ta haramta wa Ƴan Adaidaita Sahun bin wasu manyan titunan jihar baki ɗaya. Gwamnatin ta ɗauki matakin ne ta hannun  Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jihar KAROTA. Sanarwar dokar ya fito ne cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in hulɗa […]

Read More
Labarai

An Koyar Da Gwamman Matasa Kiwon Tumaki A Jihar Bauchi.

Daga Muhammad Sani Mu’azu Kimanin matasa maza da mata 35 ne aka horar kan dabarun kiwon tumaki, don dogaro da kansu da kuma yaki da talauci. Taron wanda kamfanin Ivie General Contractors da cibiyar kimiyyar dabbobi ta Najeriya ta shirya karkashin tsarinta na samar da abin yi wa marassa galihu a bangaren kiwon dabbobi a […]

Read More
Labarai

NUBASS: A karon Farko an samu Shugaban Ɗalibai ƴan asalin jihar Bauchi na kasa daga Jami’a mallakar Jiha

  Kwamitin gudanar da zaɓen Ƙungiyar ɗalibai ƴan asalin jihar Bauchi wato NUBASS a matakin ƙasa ta gudanar da zaɓen ta wanda ta sabayi duk shekara. Shugaban kwamitin zaɓen Kwamaret Abdullahi ya bayyana zaɓen a matsayin wanda ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana la’akari da irin yadda ɗalibai suka bada haɗin kai har akayi […]

Read More