Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Yayin ake cigaba da fuskantar tabarbarewar tarbiya a unguwar Dala da ke `karamar hukumar Dala a jihar Kano, al`ummar unguwar sun gudanar da wani tattaki a `karshen makon da ya gabata domin yaki da fadan Daba da shaye-sheye a unguwar.
Wani magidanci a unguwar ta Dala Baffa Mai Talata, wanda ya shiga tattakin ya fadawa wakilinmu cewa “mun shiga wani hali na fadan Daba da lalacewar tarbiyar matasa, shi yasa muka fito domin mu nuna rashin yardarmu, wannna, mun tauna tsakuwa ne don aya ta ji tsoro.
”Sadik Shazali Ali, daya ne daga cikin matasan da suka shirya tattakin ya ce yin hakan ya zama dole ne domin tin kafuwar unguwar basu taba shiga irin wannan yanayi ba, “mun shiga mawuyacin hali `Yan Daba sun damemu kusan kwanaki uku suna fada, tabbas ba za mu lamunci hakan ba, mun hada kai da hukumomin tsaro da kungiyoyi domin mu tsaftace unguwarmu, ina baku tabbacin ba zamu bari wani ya zo ya lalata mana unguwa ba.
”Da yake tsokaci ga manema labarai a lokacin tatttakin mai unguwar Dala Alhaji Daha Yusuf Garba, ya ce tattakin yana da mahimmanci sosai kuma an yi shine domin kawar da fadan Daba a unguwar.”Mun shiga wannan tattaki ne domin karfawa jama`armu gwiwa wajen yaki da miyagun ayyuka a unguwarmu ” a cewar mai unguwar.
sun fara tattakin ne daga gurin da ake kira Kwar Filin Kutare da unguwar Dala wanda a nan ne ake yawan samun fadan Daban da kuma kwacen wayoyin, inda suka ratsa ta makabatar Kuka Bulikiya gurin da ake kokawa bata garin na fakewa, daga nan suka shiga Sanka, Madigawa, Rijiya Biyu gami da Karofin Dala da `Yan Balangun Dala, Rijiyar `Yan Kada zuwa Falo `Yan Katifa, Kan Tudun Madabo da Makafin Dala zuwa Kwanar Gwammaja daga nan suka koma inda aka faro tattakin, wanda suka yi makwanni biyu da samu wani fadan Daba da ya jawo rasa ran mutum guda.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Rundunar Ƴan Sandan Jihar Kano Ta Gargadi Mazauna Jihar Kan Atisayen Harbin Bindiga A Kalebawa.
-
Ayyukan Laifin Da Aka Aikata A Kano Cikin Shekarar 2022 Sun Ragu Fiye Da 2021- Ƴan Sanda.
-
Jami’an Tsaro Sun Hallaka Ƴan Bidinga Tare Da Ragargaza Maɓoyarsu.
-
TSARO: Gwamnatin Buni ta na ci gaba da bai wa jami’an tsaro cikakken goyon baya don tunkarar matsalolin tsaro a Yobe
-
Ƴan sanda sun kuɓutar da jariri a Zamfara.