Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Babban Hafsan Sojin kasa Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya bayyana fatansa na cewa, nan ba da jimawa ba za a kawar da kungiyar Lakurawa, ta hanyar ƙarfafa hadin gwiwa da kasashen da ke makwabtaka da Nijeriya.
Oluyede ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawarsa da shugaban kasa, Bola Tinubu a Abuja.
Da ya ke jawabi a ziyarar tasa, Laftanar-Gen. Oluyede ya jaddada ƙudirinsa na inganta yanayin tsaro a Najeriya, in da ya yi alƙawarin samar da sabuwar hanyar magance matsalar rashin tsaro.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi martani kan rahoton Amnesty.
Sojojin Najeriya sun yi raga-raga da sansanonin ƴan bindiga a jihar Taraba.
Babban jami’in ya kuma bayar da bayanai kan ziyarar da ya kai a sansanonin sojoji a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.
Ya bayyana cewa, ganawarsa da dakarun sojojin ta jaddada muhimmancin kawo ƙarshen rashin tsaro a faɗin Najeriya.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.