Sanannen ɗan kwalliyar nan kuma mashahurin ɗan nishaɗi na Najeriya Okuneye Idris Olanrewaju, wanda aka fi sani da suna Bobrisky, ya bayyana cewa kwanan nan an yaudare shi a cikin wani tsarin soyayya na bugi ta yanar gizo, in da aka yaudare shi har ya rasa dala ɗari tara da tas’in.
A ranar Lahadi Bobrisky ya bayyana hakan a shafin sa na Instagram, in da ya nuna mamakin sa da kuma rashin jin daɗin sa dangane da lamarin, ya na mai cewa bai taɓa tunanin cewa zai iya faɗawa cikin irin wannan tarkon ba.
A cewar sa, wanda ya yaudare shi ya daɗe yana tuntuɓar sa ta yanar gizo, yai iƙirarin cewa ya na zaune a Amurka kafin daga baya ya koma Kanada.
A tsawon lokacin da suke magana, ɗan danfarar ya na yawan kiran sa kuma ya na nuna kamar da gaske ya na sha’awar rayuwar Bobrisky.
“Ban taɓa tunanin zan zama abokin hulɗa ga wani ba a rayuwa ta”. Inji shi.
“Wannan mutumin ya tuntube ni, muka fara magana kusan watanni da dama yanzu; ya na kirana kusan kullum; ya ce ya na zaune a Amurka amma ya koma Kanada,” in ji shi.
Bobrisky ya ce lamarin ya fara sauyawa ne lokacin da wata abokiyar hulɗa daga Amurka ta tuntube shi don talla, kuma ta ce tana son biyan kuɗi ta hanyar CashApp.
Sai ya roƙi wannan saurayi da yake magana da shi da ya taimaka masa wajen karɓar kuɗin.
“Wasu yan makwanni bayan haka, wata mata daga Amurka ta nemi talla. Ta ce tana buƙatar CashApp don biyan kuɗin ta, sai na tambayi wannan mutumin da muke magana, ya ce zai ba ni nasa; ya na karɓar kuɗin, sai ya toshe ni nan da nan,” in ji shi.
Bobrisky ya ƙara da wallafa hoton tattaunawar su da kuma hoton wanda ya yaudare shi a shafin sa, ya na gargadin masoyan sa da su yi taka tsantsan kada su faɗa irin wannan tarkon.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Gwamnatin Kano ta tabbatar da za ta yi adalci da sauraron ƙorafe-ƙorafen al’ummar da aikin magance zai zayar ƙasa zai shafa a Bulbula tare da biyan diyya
-
Buba Galadima ya ƙaryata batun komawar Kwankwaso APC da Ganduje ya yi
-
NSCDC ta tura Jami’ai 415 a Zamfara don tabbatar da tsaro lokacin bukukuwan Easter
-
Ƴansandan Najeriya Najeriya sun cafke mutum biyu kan rikicin baya-bayan nan da ya afku a jihar Filato
-
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da sabon kwamitin ƙidaya