Deprecated: Unparenthesized `a ? b : c ? d : e` is deprecated. Use either `(a ? b : c) ? d : e` or `a ? b : (c ? d : e)` in /home/martabaf/public_html/wp-content/plugins/wp-socializer/core/templates/floating-sharebar.php on line 180
Bai Kamata A Sanya Ido Kan Batancin Da Sahara Reporters Suka Yi Ga Annabi SAW Ba - Sheikh Qariballahi Kabara. - Martaba FM
October 20, 2021

Bai Kamata A Sanya Ido Kan Batancin Da Sahara Reporters Suka Yi Ga Annabi SAW Ba – Sheikh Qariballahi Kabara.

Page Visited: 891
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:1 Minute, 7 Second

Daga Suleman Ibrahim Moddibo

Shugaban mabiya darikar kadiriyya na Afrika ta yamma Sheikh Qariballahi Sheikh Muhammad Nasiru Kabara, yayi kira ga musulmai fadin duniya da su yi Allah wadai da batancin da Sahara Reporters tayi ga shugaban hallita Annabi Muhammad SAW.

Qariballahi Kabara yace “Bataci da cin zarafin Annabi irin wannan idan an gani sai dai musulmai su shiga ciki suyi ta Allah wadai su la’anceta su yi tir da su”.

Kabara, yayi kira ga mahukunta kan su dauki mataki tare da yin addu’a ga Sahara Reporters “Allah ya tarwatsa su, Allah ya la’ancesu, Allah yayi mana maganin su, Allah ya wargaza su”.

Sheikh Qariballahi Sheikh Muhammad Kabara ya bayyana hakan ne cikin wani faifan bidiyo na kai tsaye da ya wallafa a shafinsa na facebook lokacin da yake karatun Darul Hadis.

A ranar Litinin data gabata ne jaridar internet ta Sahara Reporters ambato kungiyar Yarabawa ta Afenifere tana cewa Igboho tamkar Manzon Allah ne da ya yi hijira daga Makka zuwa Madina domin kauce wa hukuncin da za a yi masa.

Sai dai Wannan firici na Sahara Reporters ya yi matukar bata ran musulmai inda suka rika yin kiraye-kiraye a kaurace wa jaridar.

Bayan nuna facin rai da musulmai suka yi ne , Sahara reporters, ta nemi gafarar musulman Najeriya kan alakanta Manzon Allah (SAW) da mai fafutukar kafa kasar Yarabawa Sunday Igboho.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us