January 31, 2023

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Bauchi: Ku Kaɗa Ƙuri’un Ku Wa Jam’iyyar PDP, Za Mu Cigaba Da Haɗa Kan Al’uma, Cewar Gwamna Bala yayin ƙaddamar da kampe

Page Visited: 69
0 0
Read Time:42 Second

 

 

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad yayi kira ga al’umar jihar da ɗaukacin ƴan Najeriya da su ƙada ƙuri’un su ga jam’iyyar PDP a zaɓukan dake tafe don cigaba da sharɓar romon dimokraɗiyya.

Yayi wannan kira ne a ƙaramar hukumar Gamawa yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe karo na biyu inda ya jaddada aniyar gwamnatin sa za ta cigaba da samar da ayyukan ɗaga darajar jiha ta hanya bunƙasa tattalin arzikin ta.

Ya yabawa masu riƙe da sarautun gargajiya kan rawar da suke takawa wajen inganta zaman lafiya da ciyar da al’uma gaba.

A jawaban su daban daban Hakiman Udubo da Gamawa yabawa salon mulkin gwamnatin Sanata Bala Muhammad suka yi kan samar da manyan ayyuka a yankin ciki har da kammala fitacciyar hanyar Bulkachuwa zuwa Udubo da gwamnatin da ta shuɗe tayi watsi da su.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *