Deprecated: Unparenthesized `a ? b : c ? d : e` is deprecated. Use either `(a ? b : c) ? d : e` or `a ? b : (c ? d : e)` in /home/martabaf/public_html/wp-content/plugins/wp-socializer/core/templates/floating-sharebar.php on line 180
Buhari Ya Umarci Hukumomin Tsaro Su Gaggauta Ceto Dukkan Daliban Da aka Sace. - Martaba FM
October 20, 2021

Buhari Ya Umarci Hukumomin Tsaro Su Gaggauta Ceto Dukkan Daliban Da aka Sace.

Page Visited: 92
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:47 Second

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci sojoji, ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su tabbatar da gaggauta ceto dukkan wadanda aka sace.

Buhari ya bada wannan umarnin ne a ranar litinin ta cikin wata takarda da Garba Shehu ya fitar a Facebook inda ya nuna damuwarsa kan harin jihohin Kaduna da Neja.

Ka kuma tabbatar da ci gaba da tura karin jami’ai dukkan yankunan da ke da matsala, shugaban kasan yayi kira ga hukumomin tsaron da su yi aikin gaggawa wurin ceto dukkan ‘yan makarantan a jihohin tare da dawo dasu gida lafiya.

Shugaban kasan ya kwatanta sace jama’an da aikin ragwancI tare da cin zarafi ga iyalai da kasar baki daya.

Buhari ya ce lamarin satar dalibai a jihohin arewa ya zama barazana ga habaka saka yara makaranta a jihohin.
Ya yi kira ga gwamnatocin jihohin da su tabbatar sun bi shirin majalisar dinkin duniya na baiwa makarantu kariya wanda gwamnatin nan ta runguma.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us