June 8, 2023

Ado Da Kwalliya

Gyaran Jiki Yana taimakawa mata ko maza wajen Sanya fata laushi da kuma dada haskawa.

Gyran Jiki na Sanya Fatar Dan Adam ta zama lafiyayya Kuma abin ban sha’awa ga kowa inda zakuga Komai yawan shekarun mutum, fatar ta na nan da kyanta.
Ado da kwalliya

Gyaran jiki dai ya samo asali ne daga Kasashen Larabawa, Sai Turawa da suke haɗa wasu Natural Organics da Chemicals kala kala don Gyra fata, Bayan su Kuma Akwai Mutane Borno (Maiduguri) anan Najeriya.

To Amma fa Gyran Jiki Sai an bi Wasu matakai idan Ana son asamu cikakken result Mai kyau Wanda duk Wanda ya daura Ido a fatar mutum yasan an Sha ma fatar wahala.

Wannan shine abu mafi muhimmanci kowa ya sani Kafin a fada zuwaga Gyran jiki.

Martaba FM Online zai Rika kawo muku hanyoyin da zaku bi don Gyra jikin ku da Kuma yin kwalliya ta kece raini.

Kadan daga Cikin Matakai na Gyran Jiki sune:

Mutum ya yawaita cin lafiyyen abinci wato Masu Gina jiki Kamar Carbohydrates, proteins, minerals da dai Sauran su.
Dole ne Mutum ya rika Shan ruwa, don ruwa Yana da matukar amfani Kuma Yana Hana fata bushewa.
Inda Hali a Rika mu’amala da ‘ya’yan itatuwa, irin su Kankana, Lemo, Ayaba da su Abarba.
Wannan yanada matukar wahala Amma Kuma yafi komai sauki, Kuma shi ake cewa maida tsohuwa Yarinya wato Atisaye ko motsa jiki.
Shine Amfani da kayan gyaran jiki irin su Kurkur, Dilka da yin su halawa.
Zamu kawo muku bayani daki daki Nan gaba.

Ado Da Kwalliya 2


Notice: Trying to access array offset on value of type bool in /home/martabaf/public_html/wp-content/plugins/social-media-share-buttons/mozedia-sharing.php on line 283

Daga Zainab Muhammad   Barkanmu da sake hadewa a wannan fili na kwalliya Ado da