Cibiyar ZITDA zata haɗa gwiwa da hukumar NADDC awani mataki na bunƙasa cibiyar ƙere-ƙere a jihar Zamfara

Page Visited: 631
0 0
Read Time:2 Minute, 21 Second

 

Babban Darakta na Hukumar NADDC masu kera motoci Malam Jelani Aliyu MFR yayi alkawarin hada hannu da gwamnatin jahar Zamfara domin a bude cibiyar koyon kera mota a Jahar Zamfara. Gusau wuri ne na musamman a yankin Arewa maso yamma.

Alh. Aliyu ya fadi hakan ne a ofishinsa lokacin da ya karbi bakuncin Babban Darakta a Hukumar Fasaha ta Zamani ta Jahar Zamfara, Muhammad Yahaya Tambura tare da Sakatare na Musamman Ga Gwamnan Jahar Zamfara, (Dr.) Lawal Umar Maradun kwanannan.

Tattaunawar ta mayar da hankali kacokan akan ababen da zasu kawo hadin kai tsakanin Hukumar ZITDA da ta NADDC a bangaroran habaka fasaha ta zamani da kuma cibiyar koyon kera mota a Jahar Zamfara.

Alh. Aliyu yayi bayani cewa umarni ne na majisar domin suyi hadin gwiwa da hukumomin gwamnatoci, dai daikun jama’a ko masu saka hannayen jari don samun cikakkar fasahar kera motoci da sauran ababenta.

Cikin dacewa, sashen kanikanci (Mechatronic department) a makarantar gwamnatin jahar ta Abdu Gusau Polytechnic Talata-Mafara, Alh. Aliyu wanda ke cike da sha’awa yace cibiyar zata iya hadin gwiwa da makarantar don bincike, zane da kuma cigaban kera samfuran motoci.

Da yake tabbatar da isowan dukkanin kayayyakin aikin da ake buƙata a cibiyar horaswan, yayi alƙawarin cigaba da bada gudummawar sa wa al’ummar jihar Zamfara dama ƙasa baki ɗaya a ɓangaren da yake da ƙwarewa.

Ya kuma bayyana farin cikin sa maras misaltuwa bisa irin gudunmawar da zauren sa ke samu daga Gwamna Bello Matawalle.

Mista Aliyu ya bayyana gudunmawar Gwamna Matawalle a matsayin na musamman wacce lashakka zata ƙara taimakawa gaya wa cibiyar wajen sanya matasa su zama masu basira a cikin al’umma.

Shugaban ZITDA Muhammad Yahaya Tambura tun da farko ya isar da farin cikin Gwamna Bello Matawalle wa Mista Jelani Aliyu bisa irin gudunmawar da yake bayarwa wajen inganta rayuwar matasa ta yadda zasu samu basira daban-daban a jihar.

Mista Tambura yace ZITDA a shirye take ta haɗa kai da NADDC don inganta cibiyar da kayayyakin na’urorin da ake buƙata.

Acewar Tambura, hukumar a jihar Zamfara tazo dai-dai da tsare-tsaren wannan gwamnati gamida shirye-shirye ciyar da jihar gaba ta hanyar sanya matasa masu baiwa da basira.

Babban maƙasudin ziyarar shine damar da shugaban NADDC Mista Jelani Aliyu ya samu na gabatar wa baƙin abun hawa na farko da aka ƙera a Najeriya.

Motar dai gaba ɗayan ta bata da sautin ƙara, bata aiki da Mai sannan tana da daɗin sha’ani bugu da ƙari zatayi tafiya mai nisa sama da kilomita 400 matuƙar anyi mata caji yadda ya kamata.

Idan aka samu wadatar motar akan tituna lashakka za’a samu sauƙin ɗumamar yanayi kuma iska zai kasance maras cutarwa hakanne yasa motar ta zama mai daɗin sha’ani.

Garzaya cibiyar horaswan dake Gusau a jihar Zamfara domin mallakar motar mai amfani da wuta sai ka zauna lafiya.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Mayan Titunan Jihar Kano Da Gwamnati Ta Haramtawa Masu Adaidata Sahu Bi.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Gwamnatin jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya  ta haramta wa Ƴan Adaidaita Sahun bin wasu manyan titunan jihar baki ɗaya. Gwamnatin ta ɗauki matakin ne ta hannun  Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jihar KAROTA. Sanarwar dokar ya fito ne cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in hulɗa […]

Read More
Labarai

An Koyar Da Gwamman Matasa Kiwon Tumaki A Jihar Bauchi.

Daga Muhammad Sani Mu’azu Kimanin matasa maza da mata 35 ne aka horar kan dabarun kiwon tumaki, don dogaro da kansu da kuma yaki da talauci. Taron wanda kamfanin Ivie General Contractors da cibiyar kimiyyar dabbobi ta Najeriya ta shirya karkashin tsarinta na samar da abin yi wa marassa galihu a bangaren kiwon dabbobi a […]

Read More
Labarai

NUBASS: A karon Farko an samu Shugaban Ɗalibai ƴan asalin jihar Bauchi na kasa daga Jami’a mallakar Jiha

  Kwamitin gudanar da zaɓen Ƙungiyar ɗalibai ƴan asalin jihar Bauchi wato NUBASS a matakin ƙasa ta gudanar da zaɓen ta wanda ta sabayi duk shekara. Shugaban kwamitin zaɓen Kwamaret Abdullahi ya bayyana zaɓen a matsayin wanda ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana la’akari da irin yadda ɗalibai suka bada haɗin kai har akayi […]

Read More