May 18, 2022

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Cikin Ƙwana Guda Ƴan Najeriya 577 Sun Warke Daga Korona Ta Kuma Kashe Mutum 7.

Page Visited: 311
0 0
Read Time:1 Minute, 23 Second

Daga Suleman Ibrahim Moddibo

Mutum 577 sun warke daga Korona cikin sa’o’i 24 wato a ranar Litinin 17 ga watan Junairun shekarar 2022 a Najeriya, wanda kuma cutar ta sake kama mutum 249 da suka fito da daga wasu jihohin Najeriya guda 14 har da birnin tarayya Abuja 15.

Hukumar da ke yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya NCDC ce, ta sanar da hakan a shafi na Twitter inda ta ce jihar  Lagos ce aka fi kamuwa da mutum 59 sai jihar Adamawa mutum 46 inda jihar Imo ta smau mutum 37 da suka kamu da cutar.

A babban birnin tarayyar Najeriya Abuja mutum 30 aka samu a ranar Litinin sai jihar Kwara mutum 14 inda jihar Rivers aka samu mutum 13, yayin da jihar Kaduna ke da mutum 10.

Sauran jihohin dai sune Taraba 9 Cross River8 da jihar Bauchi mai mutum 7 ita kuwa jihar Niger mutum 5 ne suka kamu jihar Delta da Ogun huɗu-huɗu Nasarawa na da mutum 2 Jihar Kano ce ta ƙarshe da mutum guda ya kamu a ranar.

Najeriya: Korona Ta Kashe Mutum 8 Ta Kuma Kama 301.

Mutum 50 Sun Kamu Da Korona A Jihar Gombe.

Har Yanzu Jihar Kaduna Na Fama Da Cutar Shan Inna.

Alƙaluman da hukumar ta fita sun yi nuni da mutum 7 ne suka rasa rayukansu yayin da wanda hakan ya kai ga baki ɗaya waɗanda suka mutum a Najeriya ya kai 3,110.

Zuwa yanzu an tabbatar da cutar ta kama mutum 251,178 tun daga bullar ta yayin da kuma mutum 224,629 suka warke daga Korona a cewar sanarwar.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *