Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad yayi kira ga al’umar Udubo, ƙaramar hukumar Gamawa da ma ɗaukacin jihar Bauchi da su sake marawa jam’iyyar PDP baya a zaɓukan dake tafe don ba ta damar ƙarasa ayyukan raya ƙasa da take gudanarwa don inganta zamantakewa da haɓaka tattalin arzikin jihar Bauchi.
Bala Muhammad yayi wannan kira ne da safiyar yau Alhamis a fadar hakimin Udubo yayin bikin gangamin yaƙin neman zaɓe karo na biyu.
A cewar gwamnan ayyukan gwamnatin sa a zango na farko ya sauya rayuwar al’uma da dama baya ga ɗaga darajar jihar Bauchi inda a yanzu ta tsere wa takwarorin ta a fannoni da dama.
Yace ƙarancin kuɗaɗen shiga, hantara ko makauniyar adawa ba su taɓa zama barazana ga jam’iyyar PDP ba, a saboda haka yace idan aka sake ba su dama za su cigaba da canja tarihi ta hanyar damawa da kowa cikin shan romon dimoraɗiyya a mutunce a kuma sauƙaƙe.
Gwamnan Muhammad yace a matsayin sa na ɗan hakimi ba zai yi ƙasa a guiwa ba wajen kare martabar masarautun gargajiya da a cewar sa su ne madubin kowace al’umar dake da muradin cigaba.
Ya zayyana ayyukan gyara, ginawa da kwaskwarima wa fadojin hakimai, dagatai da sarakunan yanka masu daraja ta ɗaya da kuma sabunta musu motoci a matsayin somin-taɓi na shirin gwamnatinsa na inganta raya al’adu.
Ya ƙara da cewa gwamnati me ci ta fitar dubban al’umma daga ƙuncin talauci, gyara makaranti, asibitoci da samar wa tare da ruɓanya hanyoyi a wani matakin kyautatawa da sauƙaƙa rayuwar al’umar jiha kana yace zai faɗaɗa ayyukan a zango na biyu.
Da yake marabtar tawagar gwamnan, Hakimin Udubo cewa yayi ziyarar za ta bada al’umar yankin sa damar yiwa gwamnan godiya kan fitattun ayyukan da yake gudanar wa da suka haɗa da aikin hanyar Udubo zuwa Bulkachuwa, samar da fili da tabbatar da wanzuwar fitaccen kampanin sarrafa shinkafa da sauran su.
Ya ƙara da kira ga gwanatin da ta cigaba da samar wa al’umar ayyukan more rayuwa kafin daga bisani yayi wa gwamnan fatan alheri.
Dubban masoya ne suka yi wa fada da garin Udubo tsinke don marabtar Gwamna Bala da tawagar sa tare da jaddada mubayi’ar su a gare shi.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Kotu Ta Daure Wani Matashi Watanni 15 Kan Shiga Gidan Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi M.A.
-
Amaryar Ta Rasa Idonta Daya Ne Ana Tsaka Da Bikinta Sai Dai Duk Da Haka An Daura Mata Aure Da Angonta.
-
Zargin Taimakawa Ta’addanci: SSS Sun Mamaye Hedikwatar Babban Bankin Najeriya.
-
Gwamna Bala ya sha alwashin inganta tsaro, yaƙi da talauci, yayi yaƙin neman zaɓe a Itas
-
Ƴan siyasa ku guji amfani da mimbarin Wa’azi domin biyan bukatar ku – Abdulkarim Tilde