Ecuador Ta Zargawa Qatar Mai Masaukin Baki Kwallo 2 A Raga.

Page Visited: 48
0 0
Read Time:1 Minute, 8 Second

Daga Fatima Suleman Shu’abu

Dan wasan Ecuador Enner Valencia, ne ya fara zura kwallo a ragar Qatar jim kaɗan bayan take wasan, inda daga bisani ya sake zarga musu kwallo ta biyu kafin tafiya hutun rabin lokaci.

Kwallayen da Valencia, ya ci sun bawa Ecuador damar zama ta ɗaya a tebur cikin rukunin A da maki uku rigis, inda ita kuma Qatar mai masaukin baƙi ke ta karshe a rukunin bayan rashin nasara.

Za a gane ta biyu da uku ne a rukunin tsakanin ƙasar Netherlands da Senegal idan sun buga wasansu a gobe Litinin.

Su kuwa sukunin B za su fara buga wasan su ne a ranar Litinin din inda ƙasar Ingila zata kara da Iran, yayin da ita kuma ƙasar Amurka za ta kece raini da Wales.

Qatar zata sake buga wasa ne a karo na biyu cikin rukuni a ranar 15 ga watan Nuwamba inda za ta barje gumi da Senegal, ita kuwa Ecuador wadda ke jagorantar rukunin na A da maki uku za ta buga wasanta na gaba ne da ƙasar Netherlands.

Wannan dai shine karon farko da ake buga gasar cin kofin duniya na FIFA a ƙasashen larabawa, inda za a buga wasannin a filayen wasannin guda 8 da suke ƙasar ta Qatar.

Za a rufe gasar kofin duniya ne wanda Faransa ke ɗauke da shi a ranar 18 ga watan Disambar 2022.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Wasanni

Faransa Mai Ɗauke Da Kofin Duniya Za Ta Fara Kare Kofinta A Yau Talata

Daga Suleman Ibrahim Modibbo   Ƙasar Faransa mai dauke da kofin duniya za ta yi gumurzun kare kofinta da ƙarfe 8 ɗin daren yau a ƙasar Qatar a gasar cin kofin duniyar da ke gudana yanzu haka. Faransa ta ɗauki kafin ne a shekarar 2018 a ƙasar Rasha, bayan ta yi nasara a wasan ƙarshe. […]

Read More
Wasanni

A Halin Yanzu Tunisiya Ce Ta Ɗaya A Rukunin D Bayan Ta Yi Canjaras Da Denmark A Cigaba Da Gasar Cin Kofin Duniya.

  An kai ruwa rana tsakanin ƙasar Tunisiya da Denmark wanda hakan ya kai su ga tashi babu kwallo ko ɗaya a ragar ko wace ƙasa,, abinda ke nuni da cewa ƙasashen biyu suna tsaka mai wuya cikin rukunin D. Tunisiya za ta buga wasanta na gaba ne a ranar 26 ga watan Nuwamba, inda […]

Read More
Wasanni

Saudiya Ta Fara Gasar Cin Kofin Duniya Da Kafar Dama Bayan Doke Argentina 2 Da 1.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo.   Ƙasar Saudiyya ta zama ta ɗaya a teburin C bayan yin nasara a kan Argentina da ci biyu da ɗaya a wasan farko cikin rukunin C. Argentina ce ta fara cin kwallo ta farko a bayan mintuna 20 da fara wasan ta hanyar fanareti da samu wanda ɗan wasan gabanta […]

Read More