Fara Haƙar Gangar Mai Dubu 120 A Kullum A Bauchi Zai Taimaka  Wajen Samar Da Kamfanin Takin Zamani Da Zai Rika Yin Tan Bubu 2500 Kowacce Rana.

Page Visited: 110
0 0
Read Time:1 Minute, 17 Second

Gwamnatin Najeriya ta ce kashi na farko na aikin samar da man fetur da kuma iskar gas daga yankin arewacin kasar zai taimaka mata samar da gangar mai dubu 120 kowacce rana da kuma kubik miliyan 500 na iskar gas kowacce rana a yankin, abin da zai kai ga samar da hasken wutar lantarki mai karfin megawatt 300 da kuma kamfanin samar da takin zamanin da zai rika samar da tan dubu 2 da 500 kowacce rana.

Wannan ya biyo bayan kaddamar da aikin man wanda za a rika fitar da shi zuwa kasuwannin duniya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi yau a Jihar Bauchi, sakamakon kwangilar da kamfanin man NNPC ya kulla da kamfanin NNDC da kuma AOML.

Shugaban kasa Buhari ya sanya shirin hako man daga yankin arewacin Najeriya a cikin manyan ayyukan da gwamnatinsa za ta mayar da hankali akai, duk da sukar da ke zuwa daga bangarori da dama wadanda ke cewar asarar kudaden gwamnati ake yi domin babu yawan mai da gas da Najeriya za ta ci moriyarsa a yankin.

Sakamakon aikin da aka yi a iyakokin Bauchi da Gombe, kamfanin man NNPC ya ce yawan man da Najeriya za ta samu daga yankin zai kai ganga biliyan 19, yayin da yawan iskar gas kuwa zai kai kubik biliyan 500, makamashin da yau ya zama tiraren dan goma saboda yadda ake bukatarsa a kowanne sako na duniya.

Ana sa ran wannan aiki ya taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin jihohin da abin ya shafa da arewacin kasar da kuma Najeriya baki daya.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Mayan Titunan Jihar Kano Da Gwamnati Ta Haramtawa Masu Adaidata Sahu Bi.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Gwamnatin jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya  ta haramta wa Ƴan Adaidaita Sahun bin wasu manyan titunan jihar baki ɗaya. Gwamnatin ta ɗauki matakin ne ta hannun  Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jihar KAROTA. Sanarwar dokar ya fito ne cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in hulɗa […]

Read More
Labarai

An Koyar Da Gwamman Matasa Kiwon Tumaki A Jihar Bauchi.

Daga Muhammad Sani Mu’azu Kimanin matasa maza da mata 35 ne aka horar kan dabarun kiwon tumaki, don dogaro da kansu da kuma yaki da talauci. Taron wanda kamfanin Ivie General Contractors da cibiyar kimiyyar dabbobi ta Najeriya ta shirya karkashin tsarinta na samar da abin yi wa marassa galihu a bangaren kiwon dabbobi a […]

Read More
Labarai

NUBASS: A karon Farko an samu Shugaban Ɗalibai ƴan asalin jihar Bauchi na kasa daga Jami’a mallakar Jiha

  Kwamitin gudanar da zaɓen Ƙungiyar ɗalibai ƴan asalin jihar Bauchi wato NUBASS a matakin ƙasa ta gudanar da zaɓen ta wanda ta sabayi duk shekara. Shugaban kwamitin zaɓen Kwamaret Abdullahi ya bayyana zaɓen a matsayin wanda ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana la’akari da irin yadda ɗalibai suka bada haɗin kai har akayi […]

Read More