Fetur A Arewa: Bauchi Na Maraba Da Buhari- Dr Aliyu Tilde.

Page Visited: 76
0 0
Read Time:4 Minute, 19 Second

Kaddara

Bauchi da Gombe dai kaddara ta rubuta kasancewarsu tare har abada. Farko, a Daular Usumaniya lokacin da Yakubun Bauchi da Buba Yero suka assasa masaurautunsu, an samu rashin jituwa tsakaninsu a kan ina ne iyakar kowannensu. Bayan da aka yi wani yaki a tsakaninsu har ya kai ga kashe juna, sai Muhammadu Bello a shekarar 1817 ya zartar, kuma dukkansu suka yarda, cewa kogi ya zama iyakarsu, kamar yadda ya zo a littafin The Fulani Empire of Sokoto na Johnston.

Sai kuma suka sake hadewa a karkashin mulkin Turawa da na su Sardauna, da lokacin Gowon a Arewa Maso Gabas, da tsohuwar Jahar Bauchi, kafin Abacha ya raba su a 1996. Yau, man fetur ya sake sabunta zumuntarsu a wancan kogin Kolmani wanda Sarkin Musulmi Bello ya tsayar a matsayin iyakarsu shekaru 205 da suka wuce.

Tarihi

Gobe Maigirma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kafa tarihi inda zai kaddamar da tonon mai a wadannan tagwayen jihohi, na farko irinsa a Arewacin Nijeriya. Tarihi ne saboda shekaru kusan 50 ke nan ana faman neman mai a Arewa amma bai kai ga matakin da aka cimma ba yanzu a rijiyoyin Kolmani. Da an cimma wannan matsayin tuntuni ba don gwamnatocin da suka zo bayan Marigayi Abacha sun nuna ko-oho da lamarin ba. A gaban idonmu aka rika dowowa da motocin tuno mai din a 2000 bayan Obasanjo ya hau mulki, wai ba a samu mai da yawa ba.

Da Buhari ya hau, an sake dawo da ayyukan neman mai musamman a fadamun Chadi amma dole aka dakata saboda ayyukan Boko Haram wadanda suka kashe wasu ma’aikatan Jami’ar Maiduguri da ke cikin mafarauta man. A karshe dai, an ba marada kunya, inda aka samu mai mai dumbin yawa, wajen ganga biliyan daya, a wurare kewaye da kogin Kolmani. Gobe, Shugaba Buhari zai kaddamar da hakar man, wani abu da zai dawwama a kundin nasarorin mulkinsa.

Tarihi ne kuma saboda zai kasance mafarin samun dukiya mai yawa a wannan sashin na Nijeriya musamman idan aka yi la’akari da karin bayanan kimiyya kan samuwar mai a gurare da ake da su yanzu da kuma cewa sabuwar Dokar Masana’antar Fetur ta 2021 ta samar da amfani da kashi 30% na ribar NNPC wajen farautar mai a sabbin guraren kan tudu. Da ma an gano man a fadamun Chadi da Bida, kuma suma da sannu za su kai ga matakin da na fadamar Gongola ta kai a Kolmani idan hankali ya kwanta.

Kuma tarihi ne saboda za a daina yi wa yankin Arewa kallon matsiyaciya a Nijeriya duk da cewa ita take ciyar da kasa kuma tana da al’umma da yawa, da fadin kasa da ma’adinai. Kari kan wadannan albarkatu, ita ma Arewa yanzu za ta yi kwambo da zunzurutun kudin man fetur. Da yawa daga Kudu dama suna tsoron idan Arewa da yawan mutanenta za ta arzurta, to kuma damar yi mata kallon hadarin kaji zai kare sanin cewa dukiya na zuwa da yanci, kamar yadda take zuwa da tinkaho.

Hadari

Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba. Idan ba samun shugaba mai kishin Arewa aka yi ba a zaben 2023 to duk wannan cigaba zai zama na banza. Su yan siyasa ba ko yaushe suke bin zahirin abu ba. Son zuciya ya yi yawa a lamarinsu. Haka kawai, idan mulki ya fada hannun shugaban da baya kaunar cigaban Arewa, to zai yi wa sauran aikin kafar angulu. A yanzu haka ma, masu sharhi daga kudu suna sa shakku da yamadidi a kan samuwar fetur din a Arewa. Idan aka samu shugaban kasa da zai saurare su, to za a mai da hannun agogo baya.

Tunda akwai sauran ayyuka, kamar samar da layin mai da zai hada rijiyoyin da teku ko da layin gas din zuwa Turai ko samar da matata a kusa da rijiyoyin da za ta rika tace man don amfani a gida Nijeriya, samun shugaba mai kaunar Arewa ya zama tilas a zaben da ke tafe saboda ya dora a inda Buhari ya tsaya.

To ko ma menene, Buhari ya kafa tarihi. Ya ce mafarkin shekara arba’in da ya yi a 1984 ya tabbata. Haka kuma alkawarin da ya yi lokacin zabe ya cika. Muna godiya.

Jinjina

A nan ba za mu mance da abokinmu marigayi Dr. Maikanti Baru ba, tsohon Shugaban Kamfanin NNPC wanda ya yi tsaye sai an cika alkawarin da shugaban kasa ya yi. Za a yi bikin hako man gobe ba da shi ba. Sai mu ce Allah ya jikansa da rahamarsa.

Roko

Ya zama tilas a roki Shugaba Buhari da ya jawo hankalin magajinsa kan muhimmancin cigaba da farautar albarkatun man fetur a kan tudu da kuma sauran ma’adinai ma. Karin arziki a ko’ina ne a Nijeriya amfanin yan Nijerian ne gaba dayansu. Kuma da karin ingancin zabe, mulki zai kara inganta a Nijeriya ta yanda albarkatun za su yi wa y’ay’anmu amfani, su ma su ji dadin Nijeriya kamar yanda muka yi shekaru 50 zuwa 60 da suka wuce.

Shugaba, muna maka barka da zuwa Bauchi.

Wannan ra’ayin Dr. Aliyu U. Tilde
Bauchi ne marubuci a jihar Bauchi, kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ra'ayi

Anya Kuwa Kasan Wani Tela Da Ke Ɗinka Ɗan Kamfai A Najeriya Duk Da Irin Mahimmancinsa.

  Yayin da wasu ƴan Najeriya ke kokawa da matsin taltalin arziki ake kuma nemo hanyar kawo karshensa wani mai amfani da kafafen sada zumunta Abdulwahab Said Ahmad na da ra’ayin cewa matuƙar ba a rungumi ƙananan ƙere-ƙere a gida ba to ba za a taɓa samun sauyi ba. “Ba zamu fita daga cikin halin […]

Read More
Ra'ayi

Me Ya Sa Aurenmu Ya Ke Yawan Mutuwa?

Mun dan yi wani bincike da mu ka gano wasu abubuwan da ke saurin kashe aure ko da maaurata suna son junansu, za mu fara dauko su daya bayan daya muna tattaunawa. Abu na farko da ke cikin wannan rukunan da ke kawo matsaloli a zamantakewar auranmu (hausawa) har ya kai ga rabuwa shine rashin […]

Read More
Ra'ayi

Rashin Ƙarfafawa Ke Durƙusar Da Masu Fasahar Mu A Najeriya Musamman Ƴan Arewa.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Allah ya azurta ƴan Arewa da mutane iri-iri da suke da baiwar ƙirƙire-ƙirƙire da ƙere-ƙere da yawan gaske kuma a kowane sako da lungu na ƙasar nan musamman ma a wannan yanki namu na Arewa, to amma basa samun cigaba. Suna rasa cigaba ne saboda rashin ƙarfafawa daga gwamnatoci, mawadata da […]

Read More