September 22, 2021

Gidauniyar Gwadabe Foundation ta koyarda mata Dari 500 sana’o’i hannu.

Page Visited: 217
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:1 Minute, 7 Second

Daga : Mu’azu Abubakar Albarkawa.

Anyi Kira ga masu hannu da shuni a masarautar zazzau dasu himmatu wurin taimakawa marasa karfi a cikin al’umma.

Mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ne yayi kiran, a lokacin da gidauniyar Gwadabe Foundation ta shirya yayen daliban ta wadanda aka koya masu sana’o’i domin dogaro da Kai.

Ya yabawa gidauniyar na irin namijin kokari da sukeyi wajen koyar da mata da matasa sana’o’i, bisa cewarshi tsayawa aikin gwamnati kawai ba zai gamsar ba, Don haka yace ya Zama wajibi a baiwa sana’a muhimmanci.

Mai martaban ya yi alkawarin kiran masu hannu da shuni da gwamnati a kowani mataki don ganin sun taimakawa wannan gidauniyar, inda ya sanya albarka ga wadanda aka yaye.

Da yake nashi jawabi a wurin taron Farfesa Shafi’u Abdullahi, wanda yake wakiltan Farfesa Idris Bugaje, ya yi Kira ga daliban da suyi amfani da abinda suka koya don cigaban su dama kasa baki ɗaya.

Tun farko da take nata jawabi, shugaban cibiyar Malama Khadija Gwadabe, ta godewa masarautan na Zazzau, Inda tace sun yaye dalibai dari biyar 500 wadanda suka koyi sana’o’i da dama.

Inda tayi kira ga masu hannu da shuni da su taimaka don cigaban gidauniyar, ta hanyar Samar da muhalli da kayan aiki.

Daliban da suka amfana da koyan sana’o’in sun godewa gidauniyar tare da addu’ar samun cigaba Mai dorewa.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us