September 22, 2021

Gomnatin jihar Zamfara ta mika tallafi ga wadanda Iftila’in ‘Yan bindiga ya ritsa dasu a jihar. 

Page Visited: 391
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:1 Minute, 31 Second

A Cigaba da yunkurinta na ta tallafawa Al’ummarta a kowane hauji, Gwamnatin Jihar Zamfara karkashin jagorancin Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun, ya mika tallafin kayan abinci dana amfanin yau da kullum da ma na dogaro da Kai ga al’ummomin da iftala’in yan bindiga ya fadawa a yankunan Jihar Zamfara.

 

Da take jawabi a wajen raba kayan mai baiwa, Gwamna shawara akan sha’anin jinkai da tallafawa Al’umma Hon Faika M. Ahmad ta bayyana irin fadi tashin da kullum gwamnatin Jihar take yi domin tallafawa wadannan mutane da ma sauran Al’ummar jihar.

 

Daga nan ta bayyana cewa wadannan kayan sun zo jihar Zamfara ne ta hannun hukumar kula da yan gudun hijira ta Kasa a sanadiyar koken da gwamnatin Jihar ta yi mata, Wanda ya sa hukumar ta zo Jihar har aka zagaya da ita ta ga irin abubuwan da suka Faru a Jihar.

 

Daga nan ta yi godiya ga gwamnatin tarayya akan wannan tallafi da ta kawo a Jihar, Kuma ta yi alkawarin cewa gwamnatin Jihar za ta raba kayan ga wadanda su ka cancanta.

 

Kayan abinci da su ka hada da Shinkafa,Wanke,Dawa, Goro, Masara, Garin Masara, Mangyada, Indomie, Maki.

 

Sai kuma kayan amfanin yau da kullum wadanda su ka hada da: Tabarmi, Katifu, Bukitayya, Bowls, Energy Saving Stove, Barguna, tukunyoyin Dafuwar abinci, injinan Noman Rani, da Grinding Machine.

 

Rabon kayan Wanda ya gudana a halarabar ma’aikatar da ke Samuru Gusau, ya samu halartar wakilan Hukumar karkashin jagorancin Alh. Bello M. Bello, Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli da Mu’adinai Hon Noor Isah Gusau, Kwamishinan Ma’aikatar lafiya na Jihar Zamfara. Hon. Yahaya Muhammad Kanoma, Kwamishinan Ma’aikatar Ayukkan cikin gida Hon. Sadik Muhammad Maiturare Bungudu, shugaban Kungiyar Manyan Daraktoci na Jihar Zamfara Hon. Idris Garba Rikiji, babbar Daraktan jinkai da tallafawa Al’umma Hajiya Asma’u Abdullahi Moriki da sauran jami’a n hukumar.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us