Deprecated: Unparenthesized `a ? b : c ? d : e` is deprecated. Use either `(a ? b : c) ? d : e` or `a ? b : (c ? d : e)` in /home/martabaf/public_html/wp-content/plugins/wp-socializer/core/templates/floating-sharebar.php on line 180
Gudunmawar sarakuna ga sha'anin tsaro ne kawai zai kawo mafita - Zakeer Shamsuddin - Martaba FM
October 20, 2021

Gudunmawar sarakuna ga sha’anin tsaro ne kawai zai kawo mafita – Zakeer Shamsuddin

Page Visited: 158
1 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:3 Minute, 55 Second

Daga Mu’azu Abubakar Albarkawa, Kaduna

 

Tabarbarewar tsaro a Najeriya ta sanya malaman addinai shiga addu’o’i da shawartar gwamnatin kan hanyoyin magance matsalar.

Na baya bayan nan shi ne wani sanannen malamin addinin Muslunci mai gabatar da wa’azi a kafafen watsa labarai kuma Ɗalibi a makarantar Professor’s International School Zaria da ke Jihar Kaduna Zakeer Muhammad Shamsuddin,wanda ake masa lakabi da (Young Sheikh),inda ya bayyana hakan sa’ilin wata ziyarar aiki da ya kai masarautar Ƙaraye da ke Jihar Kano.

Yayin ziyarar Zakeer Muhammad Shamsuddin ya gabatar da jawabai cikin harsunan Turanci da Larabci da kuma Hausa,tare da karanto wasu daga cikin ayoyin Alkur’ani mai girma.

Ya ce Sakamakon karuwar tashe-tashen hankula da rashin kwanciyar hankali musamman a arewacin Najeriya ya haifar da koma-baya da hanyoyin dabam-dabam da suka jibanci na bangaren tattalin arzikin kasa, noma da ilimi da harkar kiwon lafiya da kuma tarbiyyar matasa.

Yace “Tarihi ya nuna sarakuna sun bada gudunmawa wajen gina ƙasa da cigaban ta,amma yau ana ganin kundin tsarin mulkin Najeriya bai basu wani wuri na damawa a cigaban ƙasa ba.”

Zakeer Shamsuddin ya ce, a zamanin da turawa ba su san kima da darajar sarakunan gargajiya ba, domin kuwa ba su san irin tsarin da ya gudana ba ta fuskarsu, kafin zuwan mulkin Turawa.

Bayan wannan kuma kowane shugaba yana kasancewa ne bisa cancantarsa. Ma’ana, sai wanda ya cancanta zai nemi shugabanci; kamar yadda su ma jama’a suke zaben wanda suka yi imani shi ne ya fi dacewa. To, mutum ya nemi a dora shi a kan mukami domin ya cancanta, su kuma jama’a su dora masa nauyin hangen zai iya; shi yakan sanya shugabanni yin bakin kokarinsu don ganin sun kyautata wa al’ummarsu.

“Har wa yau wannan zai kasance kamar tarnaki a gare su, ta yadda ba za su yi komai da suka ga dama ba, wato babu wuce gona da iri. A kan haka lallai ne komai za su gudanar ya kasance bisa tafarkin da jama’arsu suka amince a kai.”

Sai kuma ya yi kiran ƙara samar da aikin yi ga sarakuna a kundin tsarin mulkin kasa don magance wasu matsaloli.

Daga cikin abubuwan da ya gabatar gaban Sarkin da majalisar sa,sun hada da yin kira ga ilahirin ‘yan Najeriya na cikin gida da na waje da su dinga yi wa kasar addu’ar neman zaman lafiya.

Malamin ya kuma janyo hankalin sauran masu ruwa da tsaki a kan kara himmatuwa wajen bada tasu gudunmawar wajen fargar da al’umma kan kyautata zamantakewa tsakanin dukkan ‘yan kasa.

Ya kuma bukaci gwamnati da ta taimaka wa jami’an tsaro da dukkanin kayan aiki na zamani don magance hare-haren ‘yan bindiga da masu sata da garkuwa da mutane.

Zakeer Muhammad ya nuna bukatar da ke akwai ga gwamnati wurin sanya sarakuna don magance matsalar tsaro tare da fito da sabbin hanyoyin da dabarun yaƙi da jahilci a Najeriya.

Acewarshi “Tabarbarewar tsaro a Arewacin Nigeria babbar alama ce ta yadda harkar tsaron Najeriya ta sukurkuce.”

Kuma gaza magance matsalar da dakarun da aka jibje a yankin suka yi da kuma halin ni-’yasu da ayyukan’yan bindiga suka jefa al’ummar yankin abubuwa ne a fili.

Tun farko da yake nashi jawabin, Shugaban makarantar Professor’s International School Zaria Malam Hamza Jibrin, ya ce sun zo Masarautar Ƙaraye ne domin amsa gayyatar Mai Martaba Sarkin Ƙaraye Dr Ibrahim Abubakar da ya bukaci hukumar makarantar ta je gaban sa domin yi masa bayani kan makarantar da nasarorin da aka samu tun lokacin kafa ta zuwa yanzu.

Ya ce kasancewar Masarautar ɗaya daga cikin daulolin musulunci a ƙasar Hausa kuma Sarkin Ƙaraye ɗaya ne daga cikin iyayen makarantar , kuma gare su abin alfahari ne kuma ba za su mance da irin shawarwari da mai martaba sarkin ke basu ba don bunƙasa harkar koyarwa a makarantar.

Da yake maida jawabi,Sarkin Ƙaraye Dakta Ibrahim Abubakar ya jinjina musu bisa nasarorin da aka samu a makarantar tun lokacin kafa ta zuwa yanzu,ya kuma yi fatan za’a su cigaba da ɗaurawa kan ƙoƙarin da suke na samar da nagartaccen ilmin zamani da na addini.

A ɓangaren shi kuwa,ya yi alƙawarin cigaba da bada gudunmawa ta kowace fuska don cigaban makarantar.

Makarantar Professor’s International School dai an kafa ta ne a garin Zariya da ke Jihar Kaduna don samar da nagartaccen ilmin zamani da na addini, kuma an yaye dalibai masu yawa da suka haddace Alqur’ani mai girma da kananan shekaru.

Kuma suna koyarwa a bangarori daban-daban kamar matakin kananan yara a Pre-Nursery da Primary da kuma Sakandare a bangaren kwana da jeka ka dawo.

Kuma akwai bangare na musamman da ake koyar da Alqur’ani mai girma da darussan addinin Musulunci.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us