September 22, 2021

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Gwamnan Jihar Gombe ya rabawa Shugabannin ƙananan hukumomi 11 Motoci

Page Visited: 159
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:2 Minute, 9 Second

 

A safiyar Alhamis din nan ne Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya gabatar da sabbin motocin ƙirar GAC ​​Sedan (Saloon) ga shugabannin ƙananan hukumomi 11 a jihar.

Yayin gabatar da bikin a gidan gwamnatin Gombe, Gwamna Inuwa Yahaya ya ce yanke shawarar sayen motocin ya zama wajibi don bawa shugabannin ƙananan hukumomi damar gudanar da ayyuka ga jama’a.

Gwamnan ya umurce su, su yi amfani da motocin yadda ya kamata, yana mai cewa tun da an samar musu motocin, za su iya isa duk yankunan dake karkashin kulawar su, kuma su yi aiki yadda ya kamata.

Gwamna Inuwa Yahaya ya kuma jaddada kudirin gwamnatin sa na tallafawa kananan hukumomi a jihar don yi wa jama’a aiki yadda ya kamata.

Yace “Ina matukar farin ciki kuma ina matukar jin dadin ingancin wadannan sabbin motocin da muka bawa Shugabannin kananan hukumomin mu. Bayan shigowar mu, sai muka fahimci cewa shugabannin kananan hukumomin suna samun matsala sosai ta fuskar zirga-zirga wadda hakan ke haifar da wahalhalun daidaita ayyukan kananan hukumomin saboda kalubalen da suke fuskanta game da harkokin sufuri.

“A wannan gaɓar ce ma’aikatar kula da ƙananan hukumomi da harkokin Masarautu ta turo buƙata kuma ta samu amincewar mu don samar da motocin, don haka ina taya ku murna kan wannan ci gaba”.

“Bari in tunatar da jama’a cewa mun fara ne da sayan motocin ga hukumar bunkasa kiwon lafiya a matakin farko. Inda muka bawa dukkan shugabannin kula da lafiya a matakin farko na ƙananan hukumomi motoci ƙirar 4×4 pickup ta yadda za su inganta ayyukan su, don yin abubuwan da suka dace wadda kuma tuni hakan ya fara haifar da ɗa mai ido.

“Kamar yadda yake a yau, duk mazabun mu, 114 suna da a kalla cibiyar kula da lafiya matakin farko guda daya a fadin jihar inda ake tabbatar da kulawar jinya dasu ga jama’a; don haka muna sa ran suma shugabannin suyi hakan domin mu samu aiki mai matukar kyau da kuma isar da sako mai ma’ana wanda zai taimaka wajen ci gaban jihar”.

Tun da farko, Kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin Masarautu, Hon. Ibrahim Dasuki Jalo, wanda ya gabatar da motocin ga Gwamnan don dubawa da kuma gabatar da su ga wadanda suka ci gajiya, yana tabbatar da inganci da ƙarkon motocin.

Da yake jawabi a madadin wadanda suka ci gajiyar, Shugaban karamar hukumar Gombe, Alhaji Aliyu Usman Haruna wanda kuma shi ne Shugaban kungiyar ƙananan hukumomin Najeriya (ALGON), na Jihar Gombe, ya yabawa Gwamnan bisa wannan karimcin da ya yi kuma ya yi alkawarin amfani da su kan manufar da aka samar da su.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us