June 27, 2022

Gwamnan jihar Jigawa ya karbi riga kafin Cutar COVID-19.

Page Visited: 323
0 0
Read Time:40 Second

Daga: Salihu A Auwal Jigawa

Gwamnan jihar Jigawa Badaru Abubakar tare da Mataimakinshi Sunyi allurar Rigakafin cutar Covid-19.

 

Ajiya laraba ne Gwamna Badaru Abubakar na jigawa da mataimakinsa Umar Namadi tare da shugaban gamaiyar kungiyoyi na jihar jigawa comarad Muhammad Musbahu Basirka duk sun amshi alluran riga kafin.

 

Gomnan dai tareda sauran jami’an Sun karbi Allurar rigakafin covid-19 a gidan gwamnatin jihar Jigawa.

 

Haka zalika shugaban gidajen redio na jihar Jigawa Comared Mati Ali anyi masa allurar rigakafin.

 

Komitin karta kwana wato task force kan Cutar COVID-19 sunyi kira da babbar murya ga shugabannin al’umma da suyiwa mabiyansu cikakken bayanin rashin Illar dake tattareda Allurar cutar Corona virus.

 

Gwamnan Badaru Abubakar yayi kira da babbar murya ga al’uma domin ganin kowa yakarbi rigakafin.

 

 

 

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *