June 8, 2023

Gwamnan Kano Ganduje Ya Yi Ganawar Sirri Da Sanata Shekarau Na PDP.

Page Visited: 100
0 0
Read Time:1 Minute, 12 Second

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Rahotanni daga jihar Kano a Najeriya na cewa Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, ya yi wata ganawar sirri ta kusan rabin sa a da Malam Ibrahim Shekarau, Sanatan Kano ta Tsakiya a gidan sa da ke Munduɓawa.

Sun yi ganawar ne a safiyar Juma’ar nan bayan gwamnan ya yiwa Ibrahim Shekarau rakiyar bazata zuwa gida daga maƙabarta inda aka yi jana’izar wani ɗan kasuwa Marigayi Sani Dahiru Yakasai SDY da ya rasu a jiya.

Freedom Radio da ke jihar Kano ta rawaito cewa an binne marigayin ne a makabartar Tarauni da misalin karfe goma da mintuna biyar na wannan safiya.

To sai dai kuma har zuwa yanzu babu wani cikakken bayani daga ɓangaren Shekarau ko Gwamnan kan abinda suka tattauna, duk da cewa wasu sun fara alaƙanta ganawar da zaɓen gwamna da ke tafe a ranar Asabar ta makon gobe ba.

Malam Ibrahim Shekarau, ya fice daga jam’iyyar APC mai mulkin Kano zuwa NNPP yana mai zargin yi masa rashin adalci inda daga bisani ya fice daga jam’iyyar NNPP, inda nan ma ya zarge su da rashin adalci, al’amarin da ya sanya shi ya koma jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya da jihar Kano.

A jihar Kano dai akwai ƴan takarar kujerar gwamnan jihar da dama, to amma takarar tafi zafi ne a tsakanin Jam’iyyar APC mai mulkin Kano wadda mataimakin gwamnan jihar Nasiru Yusuf Gawuna, ke mata takara, da NNPP wadda Abba Kabiru Yusuf, ke mata takara.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *