June 8, 2023

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Gwamnan Kogi Ya Sha Alwashin Ɗaure Duk Wanda Yaƙi Karɓar Tsofaffin Kuɗaɗe.

Page Visited: 118
0 0
Read Time:55 Second

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, ya yi barazanar kamawa tare da gurfanar da waɗandake ƙin karbar tsofaffin takardun kuɗaɗen Naira.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo, ya fitar a Lokoja.

Sama da mako guda ne dai kotun kolin ta yanke hukuncin ci gaba da amfani tsofaffin takardun kudin Naira na N1000, N500 da N200 tare da takardun kudi da aka sabunta har zuwa Disamba 2023.

Gwamnan ya bayyana cewa ba za su lamunci kin karɓar tsohon kudin da wasu ke yi ba, bayan hukuncin kotun ƙoli.

“Wannan gwamnatin ba za ta tsaya kallon yadda wasu mutane da ‘yan kasuwa ke ci gaba da kin karɓar tsohuwar takardar Naira ba, duk da hukuncin kotu da ta tabbatar da amfani da su.

“A gare mu, kin amincewa da tsofaffin takardun Naira, rashin biyayya ne ga hukuncin da Kotun Koli ta yanke, wanda ya kamata a daƙile.

“Duk wanda ya ki karɓar tsohuwar takardar naira, a kai rahoto ga jami’an tsaro da na gwamnati domin a kama su da kuma gurfanar da su a gaban kuliya.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *