August 8, 2022

Gwamnati Ta Ayyana Masu Amfani Da Makami Suna Kwacen Waya Amatsayin Yan Fashi- YAPS.

Page Visited: 413
0 0
Read Time:2 Minute, 23 Second

Daga Suleman Ibrahim Moddibo

An bukaci gwamnatin jihar Kano da majaliasar dokokin jihar su ayyana masu amfani da makami wajen kwacen waya amatsayin yan fashi da makami, tare da zartar musu da hukunchi daidai da yan fashi da makami.

Wata kungiya ce ta matasa masu rajin kawo karshen kwacen waya a jihar Kano ta bukaci hakan a yayin wani taro da suka shirya domin lalubo hanyar da za a kawo karshen kwacen waya.

Shugaban kungiyar Matasa Masu Rajin Kawo Karshen Kwacen Waya Ta Jihar Kano wato YAPS, Abdulwahab Said Ahmad, ne ya bayyana hakan, inda ya ce la`akari da yadda lamarin kwance waya da sauran wasu matsaloli ne suka muka shiya wannan zaman, “na farko mun yi kira ga gwamnati da majalisar dokokin jahar kano da su ayyana masu amfani da makami suna kwacen waya amatsayin Yan Fashi da makami, tare da zartar musu da hukunchi daidai da Yan fashi da makami kamar yanda doka ta tanada a tsarin dokokin jahar Kano da kasa Baki daya.”

“Sannan mun bukaci gwamnati ta umarci hukumar tace fina finai ta jahar Kano, da ta dakatar da masu shirya fina finan hausa a jahar daga shirya fina finaI masu nuna yanda ake taaddanchi da gurbata tarbiya,” inji shi.

A cewarsa yin haka da masu shirya fina-finai suke yana taka rawa wajen koya kwacan waya “domin irin wannan fina finan suna taka muhimmiyar rawa wajan gurbata tarbiyar matasa da kuma nuna dabarun kwacen waya da sauran laifuka.”

“Na biyu mun kuma yi kira ga majalisar malamai da limamai ta jahar Kano su cigaba da wayarwa da jama`a kai akan hakkin bawa yara tarbiya a musulunci da kuma hukuncin da ubangiji ya tanada ga duk uban da ya ba da gudunmawa wajan lalacewar tarbiyar ‘yayansa, ta hanyar amfani da mambarin juma`a da majalisin karatuttuka.”

“Na uku mun kuma yi kira ga masarautar jahar Kano data umarci hakimai, dagatai da masu unguwanni da lallai su samar da kwamitin tsaro acikin dukkan unguwannin jahar Kano domin taimakawa jami`an tsaro da bayanan sirri,” a cewar shugaban kungiyar.

Abdulwahab Said Ahmad ya cigaba da cewa, “mun ja hankalin kafafan yada labarai dake jahar Kano, da su samar da shirye shirye na musamman domin wayarwa da al`umma kai da dabarun kare kai domin samun nasarar dakile wannan annobar ta kwacen waya a jahar Kano.”

Mun kuma ja hankalin yan siyasa da suji tsoron Allah akan gudunmawar da suke bayarwa wajan dakile hukuma na samar da hukunchi akan masu aikata laifuka, acewar shugaban yin hakan babban koma bayane ga tarbiya da tsaron wannan jaha tamu me albarka.”

Wannan dai na zuwa ne yayin da al`ummar jihar Kano ke cigaba da kokawa da yadda yan kwacen waya a jihar ke cigaba da zafafa ayyuakansu, said ai kuma hukumomi ne cewa suna iya kokarinsu wajen kawo karshen matsalar kwacen waya a Kano.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *