Daga: Suleman Ibrahim Modibbo
Cikin jawabin da ya yi ga yan Najeriya a shafinsa na facebook kan ranar da ƙasar bikin ranar dimokradiyya tsoton mataimakin shugaban ƙasar Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasar a babban zaben ƙasar da ke tafe na shekarar 2023 Atiku Abubakar ya buƙaci ƴan Najeriya da su hada kai wajen kawar da jam`iyyar APC mai mulkin ƙasar.
“Mu hada kai tare da samun adadin da za mu kori APC jam’iyyar bacin rai da ranto kudade, ya kamata mu sani cewa, a yanzu haka bashin da ake bin Najeriya ya kai naira tiriliyan 41, kuma muna da kasa da dala biliyan 40 a asusun rararmu,” in ji shi.
Ya kuma kara da cewar “a bayyane take karara gwamnatin Buhari ta kawo mana shugabanci mafi muni ga kasarmu, inda rashin tsaro, rarrabuwar kawuna, rashin adalci, rashin aiyukan yi, tabarbarewar habakar tattalin arziki da hauhawar farashi ke mana barazana baki daya.”
“Sakamakon wannan yanayi da aka shiga, a shekara mai zuwa za mu yi watsi tare da korar gwamnatin APC mara manufa, tsari da kan gado,” a cewarsa.
“Jam’iyya mai mulki da ke hana mutane damarmaki, ba za ta taba daga martaba da habaka kasa mai bambance-bambance irin tamu ba.”
“APC da ta gaza yin gaskiya ga jama’arta, ta kuma gaza cika alkawururrukan da ta dauka a lokacin yakin neman zabe, da suka shafi tsaro, habaka tattalin arziki da yaki da cin hanci da rashawa; bai kamata a sake zabar ta don ta sake lalata wani wa’adin mulki, ci gaba da kashe kasa da lalata ta ba.”
Atiku abubakar ya kuma ce, “wannan ne dalilin da ya sa dole a kori ‘yan siyasar APC ta hanyar nuna musu damar samun mulki ta hannun jama’a.”
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƙirƙirar gata wa matan tsoffin shugabanni bayan sun bar mulki bai dace ba — Maiwada Dammallam
-
Gwamnatin jihar Bauchi ta bunƙasa ilimi a matakin farko ta hanyar saka wa masu hazaƙa
-
Zaman Dauda Gwamnan Zamfara Zai Ƙara Farfado Da Harkar Ilimi A Jihar.
-
Buhari: Don Allah Ka Dakatar Da Gwamnan CBN- Dr.Tilde.
-
Anya Kuwa Kasan Wani Tela Da Ke Ɗinka Ɗan Kamfai A Najeriya Duk Da Irin Mahimmancinsa.