Gwamnatin Kano Ta Ƙaryata Cewar Ganduje Ya Naɗa Naburaska Mai Ba Shi Shawara A Ɓangare  “Farfaganda”

Page Visited: 4271
0 0
Read Time:54 Second

Daga Suleman Ibrahim Moddibo

Gwamnatin Kano ta musanta bawa jarumin fina-finan Hausa na Kannywood, Mustapha Naburaska, matsayin mai bawa gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, shawara a bangaren farfaganda.

Babban mai taimakawa gwamnan a ban kafafen sada zumunta Abubakar Aminu Ibrahim ne ya tabbatarwa da Martaba FM hakan.

Abubakar ya ce “ba gaskiya bane ba ya dai naɗa shi mai ba shi shawara a kan ƴan wasan Hausa ƴan Kanywood amma ba farfaganda ba.”

Tin da farko dai jaridar Aminiya ce ta rawaito labarin inda ta ce “gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya nada fitaccen jarumin nan na masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Mustapha Naburaska a matsayin mai ba shi shawara kan ‘farfaganda’.

Jaridar ta kuma ce “Jarumi, kuma mai shirya fina-finai a masana’antar, Falalu A. Dorayi ne ya sanar da nadin a shafinsa na Instagram ranar Lahadi, inda ya taya shi murnar samun matsayin.”

“Falalu ya ce an gudanar da bikin nadin ne yayin wata walimar cin abincin dare da ta gudana a Gidan Gwamnatin Kano da maraicen Asabar,” kamar yadda jaridar ta ambato.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Wasanni

Faransa Mai Ɗauke Da Kofin Duniya Za Ta Fara Kare Kofinta A Yau Talata

Daga Suleman Ibrahim Modibbo   Ƙasar Faransa mai dauke da kofin duniya za ta yi gumurzun kare kofinta da ƙarfe 8 ɗin daren yau a ƙasar Qatar a gasar cin kofin duniyar da ke gudana yanzu haka. Faransa ta ɗauki kafin ne a shekarar 2018 a ƙasar Rasha, bayan ta yi nasara a wasan ƙarshe. […]

Read More
Wasanni

A Halin Yanzu Tunisiya Ce Ta Ɗaya A Rukunin D Bayan Ta Yi Canjaras Da Denmark A Cigaba Da Gasar Cin Kofin Duniya.

  An kai ruwa rana tsakanin ƙasar Tunisiya da Denmark wanda hakan ya kai su ga tashi babu kwallo ko ɗaya a ragar ko wace ƙasa,, abinda ke nuni da cewa ƙasashen biyu suna tsaka mai wuya cikin rukunin D. Tunisiya za ta buga wasanta na gaba ne a ranar 26 ga watan Nuwamba, inda […]

Read More
Wasanni

Saudiya Ta Fara Gasar Cin Kofin Duniya Da Kafar Dama Bayan Doke Argentina 2 Da 1.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo.   Ƙasar Saudiyya ta zama ta ɗaya a teburin C bayan yin nasara a kan Argentina da ci biyu da ɗaya a wasan farko cikin rukunin C. Argentina ce ta fara cin kwallo ta farko a bayan mintuna 20 da fara wasan ta hanyar fanareti da samu wanda ɗan wasan gabanta […]

Read More