Gwamnatin Kano Ta Kama Mushen Dabbobi A Manyanka.

Page Visited: 1798
0 0
Read Time:1 Minute, 9 Second

Hukumar Kare Hakkin Masu Sayen Kayayyaki ta Jihar Kano (CPC), ta ce ta kama mushen dabbobi a mayankar ’Yan Awaki da ke Unguwa Uku a karamar hukumar Tarauni da ke jihar.

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa jami’in hulda da jama’a na hukumar, Musbahu Yakasai, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ga manema labarai ranar Talata.

Ya ce, hukumar ta samu labarin dabbobin ne da misalin karfe 6:00 na safiya yayin da Babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar kan ingancin kayayyaki, Alhaji Salisu Muhammad, ya wakilci mai rikon shugabancin hukumar Baffa Babba Dan’agundi, a wajen kamen.

“Mun sami labari daga wasu mutane masu kishi cewa an kawo matattun dabbobi a mayankar da suka hada da raguna da awaki bayan an yanka su a wani waje.

“Nan take tawagarmu ta dauki mataki tare da kame dabbobin a kokarinmu na kare mutanen Kano daga amfani da kayayyakin na jabu da lalatattun kayayyaki”.

Ya ce hukumar ta gayyaci wani likitan dabbobi domin gwada dabbobin ko sun dace da cin namansu tare da tabbatar da ko da gaske ne yawancinsu sun mutu kafin a yanka su.

Haka kuma ya kara da cewa hukumar za ta yi maganin masu laifin yadda ya kamata.

Sanarwar ta kuma ruwaito cewa Babba Dan-Agundi ya bukaci mahauta da su daina aikata irin wannan mummunar ta’ada ko kuma su fuskanci fushin hukuma.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Matashi Ya Yiwa Mahaifin Budurwarsa Mummunan Rauni Bayan Ya Hana Shi Kaiwa Dare Idan Yaje Zance.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Saurayin ya yiwa mahaifin budurwarsa rauni ne bayan da baban budurwar tasa ya hana shi kaiwa dare idan yaje zance a garin Ɗan Hassan, da ke ƙaramar hukumar Kura ta jihar Kano da ke arewacin Najeriya. Arewa Radio ta rawaito cewa, an jiwa mahaifin budurwar raunine bayan da ya umarce saurayin […]

Read More
Labarai

Sojoji sun sake yin juyin mulki a kasar Burkina Faso.

Sojoji a Burkina Faso sun hamɓarar da shugaban gwamnatin sojan ƙasar, Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba a yau Juma’a, bayan ya hau mulki a watan Janairun da ya gabata. Wata sanarwa da sojojin suka karanta ta kafar talabijin ɗin ƙasar ta ce an rufe dukkan iyakokin ƙasar na ƙasa daga daren yau. Haka nan sun […]

Read More
Labarai

Lauyan Gwamnatin Kano Ya Nemi Kotu Ta Yiwa Abduljabbar Hukunci.

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci dake Kofar Kudu Karkashin me Shari’a Ibrahim Sarki Yola ta ce za ta ayyana ranar da za ta yanke hukunci kan karar da Gwamnatin Jahar Kano ta shigar da Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara bisa zarginsa da kalaman batanci. Yayin zaman na Yau dukkannin bangarorin Shari’ar sun gabatar da Jawabansu na karshe […]

Read More