Deprecated: Unparenthesized `a ? b : c ? d : e` is deprecated. Use either `(a ? b : c) ? d : e` or `a ? b : (c ? d : e)` in /home/martabaf/public_html/wp-content/plugins/wp-socializer/core/templates/floating-sharebar.php on line 180
Gwamnatin Kano Ta Sanya Ranar 10 Ga Watan Yuli A Matsayin Ranar Mukabala Da Abduljabbar. - Martaba FM
October 20, 2021

Gwamnatin Kano Ta Sanya Ranar 10 Ga Watan Yuli A Matsayin Ranar Mukabala Da Abduljabbar.

Page Visited: 175
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:46 Second

Daga Suleman Ibrahim Moddibo

Cikin wata zantawar Kwamishinan harkokin addinai na jihar Muhammad Tahar Adamu wanda ake kira Baba Impossible da BBC Hausa a ranar Alhamis ya bayyana ranar 10 ga watan Yuli a matsayin ranar mukabalar da za a yi tsakanin fitaccen malamin nan Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da wasu malaman jihar.

Ya ce za a gudanar da mukabalar ce ranar Asabar 10 ga watan nan na Yuli a Hukumar Shari’a da ke birnin na Kano.

Muhammad Tahar ya ce tuni ya mika takardar gayyatar yin mukabalar ga malamin da malaman da za su fafata da shi.

Wasu malamai na zargin Abduljabbar din da yin batanci ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

Wanda bayan gwamnatin ta samu korafi kan hakan daga al’ummar jihar gwamanati ta hana shi yin wa’azi tare da rufe masallacinsa da kuma hana sanya karatunsa a kafafen watsa labarai da kafafen sadarwa na zamani bayan samun umarnin wata kotu a jihar.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us