Gwamnatin Najeriya Ta Umarci Shugabannin Jami’o’i Su Buɗe Makarantu.

Page Visited: 523
0 1
Read Time:1 Minute, 2 Second

Gwamnatin tarayya ta umarci shugabannin jami’o’i (VCs) da su sake bude makarantu tare da baiwa dalibai damar komawa karatu.

Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun daraktan kudi da asusun kula da jami’o’in kasar, NUC, Sam Onazi, a madadin babban sakataren hukumar, Farfesa Abubakar Rasheed a Abuja a yau Litinin.

Wasikar, wacce aka aika zuwa ga dukkan shugabannin jami’o’in, Dattawan jami’o’in tarayya da ciyamonin majalisun gudanarwar jami’o’in tarayya, sun yi kira gare su da su sake bude jami’o’in domin a ci gaba da karatu.

Kotu Ta Umarci ASUU Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Ke Yi Tsawon Watanni 7.

ASUU: Dan Me Za A Ce Shugaban Kasa Ya Yi Watsi Da Ilimi? – Garba Doya.

Ƴan Sandan Bayelsa Sun Kama Wani Ƙasurgumin Mai Sace Mutane.

“Ku tabbatar da cewa ‘yan kungiyar ASUU nan da nan suka koma/fara lakcoci; maido da ayyukan yau da kullun na jami’o’i daban-daban”, in ji wasikar.

Ƙungiyar ASUU ta shiga yajin aikin ne tun ranar 14 ga watan Fabrairu domin matsa wa jami’o’in da ke neman ganin an inganta kudade, da batun albashin malaman jami’o’i da dai sauransu.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ilimi

Ta Leƙo Ta Koma: Gwamnatin Najeriya Ta Janye Umarnin Da Ta Bayar Na Buɗe Jami’o’i.Q

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Gwamnatin tarayya ta janye umarnin da ta ba shuganannin jami’o’i na su koma bakin aiki. Tinda farko a safiyar ranar Litinin ɗin nan gwamnatin ta bawa shugabannin jami’o’in umarnin buɗe makaratun cikin wata wasiƙa mai lamba NUC/ES/138/Vol.64/135 da kungiyar NUC ta fitar. To sai dai ta yammacin ranar wata wasiƙar ta […]

Read More
Ilimi

Kotu Ta Umarci ASUU Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Ke Yi Tsawon Watanni 7.

Kotun ma’aikata ta sawa kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU birki kan yajin aikin da ta ke yi tsawon watanni. Da yake gabatar da hukunci kan bukatar wucin gadi da gwamnatin tarayya ta nema, Mai shari’ah Polycarp Hamman ya hana kungiyar ASUU ci gaba da yajin aiki har zuwa lokacin yanke hukunci kan shari’ar. Mai […]

Read More
Ilimi

Makarantun Wuni Na Mata-Zalla A Jahar Bauchi Za Su Fara Ran 25 Ga Satumba

Majalisar Zartarwa ta Jahar Bauchi (Bauchi State Executive Council) a zaman da ta yi jiya, 9 Satumba, 2022, wanda Gomna Bala Abdulkadir Mohammed ya shugabanta, ta sahhale wa Ma’aikatar Ilimi fito da tsarin da zai hana cakudewar dalibai maza da mata a makarantun sakandaren wuni a Jahar, duk inda haka, ko lokacin da haka, zai […]

Read More