September 22, 2021

Gwamnonin Kudancin Najeriya Na Son Shugaban Kasa Ya Fito Daga Yankin Kudu.

Page Visited: 129
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:36 Second

Kungiyar gwamnonin jihohin kudancin Najeriya ta ce dole shugabancin Najeriya ya kasance karba-karba daga yankin arewaci zuwa kudanci.

Kuma kungiyar tana son shugaban kasa da za a zaba nan gaba ya fito daga yankin kudancin Najeriya.

Kungiyar ta tsayar da matsayar ne bayan kammala taron gwamnonin kudancin ƙasar a ranar Litinin a Lagos.

Gwamnonin kuma sun amince da wasu bukatu da suke son a aiwatar da suka shafi tsaro da yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima da kuma dokar man fetur.

A sanarwar da gwamnonin jihohin kudancin kasar suka fitar ta jaddada bukatar tabbatar da mulki ya dawo kudancin kasar kan abin da gwamnonin suka kira tabbatar da adalci tare da sake jaddada goyon baya ga hadin kan Najeriya.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us