September 22, 2021

GWMANA BALA A SHEKARA BIYU: Karfe duk karfe ne…. (II)

Page Visited: 365
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:2 Minute, 7 Second

Daga Lawal Mu’azu Bauchi

 

Duk da cewa shekarar 2020 ta zo cike da Kalubalen tattalin arziki da kuma cutar corona da ta addabi duniya, Hausawa suka ce me zuciya ake fadawa biki ba me zani ba.

Gwamna Bala Muhammad bai yi Kasa a guiwa ba wajen cigaba da samar da ayyukan cigaba da kawo sauyi ga rayuwar al’umar jihar Bauchi ba.

An ware kaso me tsoka cikin kasafin kudin shekarar 2020 kuma nan take aka fara samar da sauye sauye na musamman cikin matakan inganta tare da farfado da martabar ilimi.

Fitattu cikin ayyukan Gwamna Bala cikin shekarar 2020 sun hada da:

1. Janairu: Samar da kujerun zama da kuma kayan saukaka koyo da koyarwa na daruruwan miliyoyin nairori.

2. Febrairu: Cikin wannan wata Sanata Bala Muhammad ya gina tubalin ginin da tarihi zai rubuta sunan sa da alkalamin zinare inda aka kaddamar da aikin gina gidaje dubu biyu a masarautun Bauchi, Katagum, Misau, Jamaare, Ningi da kuma Dass, ayyukan an ware biliyoyin nairori don gudanar da su da zummar samar da gidajen kananan ma’aikata akan farashi me rahusa.

3. Maris: Gwamnati ta samar da kekunan dinki da ta rabawa teloli sama da arbain baya ga biya musu kudaden haya cikin matakan horas da mata da matasa masu kananan sana’oin hannu.

An sabunta wutar tituna cikin fadar jiha da kuma gyara wadanda suka shafe shekaru ba sa aiki duk cikin wannan wata.

4. Afrilu: Gyaran wutar lantarki Makara Huta da kuma Sabon layi wadanda dukkanin su aka sanyawa sabbin injunan wuta.

Har wa yau Gwamna Bala Muhammad ya kaddamar da gina sansanin alhazan jihar a Durum, aikin wanda shine irinsa na farko a shiyyar arewa maso gabas.

5. Mayu: samar da injunan wuta a unguwar Baraya da kuma fadada lantarki a Magama-Gumau, karamar hukumar Toro.

6. Yuni: Sabunta dakin binciken/karatu na jiha zuwa na zamani.

Gyara da kwaskwarima wa wasu daga cikin manyan asibotocin jiha da kuma samar kayan yaKi da yaduwar cutar corona.

Bayar da gudummawar jari da kayan amfanin gona wa mata dari biyu da matasa dari a fadin jiha.

7. Yuli: Aikin hanyar Gwan-gwan-gwan zuwa Bakaro, Kofar Dumi -Malam Goje-Bakin kura zuwa Muda Lawal.

Gyaran gidajen malamai, dakunan karatu da wuraren kwanan dalibai a sakandiren gwamnati da ke Katagum.

Samar da lantarki a da injin wuta a Maje, karamar hukumar Ningi.
Gina bayi da daruruwan famfunan burtsatse a kananan hukumomin Alkaleri, Gamawa, Itas Gadau, Bauchi, Misau, Zaki da Jamaare.

Cigaba na nan tafe…

Lawal Muazu Bauchi
Me tallafawa Gwamna Bala Muhammad kan kafafen yada labarai na zamani

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us